
ANYA UBANA NE
PAGE 8
Daga: Hausa Novel Dot Com
Littafin: ZULFA’U SA’EED IBRAHIM
Kazar ta dunga yaga tana ci, har sai da ta ƙoshi sosai, sannan ta bi da Hollandia mai sanyi. Ta miƙe tana cewa:
“Washh Ashraf, bacci nake ji.”
Mamaki ya cika zuciyarsa. A ganinsa, amarya ya kamata ta kasance mai kunya, amma wannan kam sam babu shi. Ya nuna mata gado. Ta miƙe tana ɗan karkada jikinta, ta kwanta.
Bai yi mamaki ba sai da ya kwanta, ya ga ta mirgina ta dawo jikinsa, ta matse shi sosai tana masa wasa a jiki, tana hura masa iska a fuska. Suka ɗauki lokaci suna soyayya kafin ya shige ta. Duk da ba lokaci ɗaya ya faru ba, amma ya fahimci ba shi ne na farko ba.
Tun farko tana jin daɗi, daga baya ta fara jin wahala. Bai sauka daga kanta ba sai kusan asuba. Bacci mai nauyi ya ɗauke ta.
Shi kuwa ya miƙe yana jin haushi, ya shiga bayi ya yi wanka. Bayan ya fito ya kwanta, amma bacci bai ɗauke shi ba. Tunani kawai yake yi—me ya sa wasu mata ba su san darajar kansu ba? Wannan tunanin ya sa tsanar ta fara shiga zuciyarsa.
Kiraye-kirayen sallar Fajr suka fara. Ya tashi ya yi alwala, ya yi nafila, sannan ya tafi masallaci.
Da ya dawo, ya same ta tana bacci. Haushi ya ƙara kama shi, ya ɗan daka mata tsawa. Ta farka a firgice tana goge idanu, ta ce:
“Haba dan Allah honey, duk wahalar da ka bani jiya bai isheka ba, sai ka hana ni barci?”
Ya daure fuska ya ce:
“Ba surutu nake so ba. Ki tashi ki yi wanka ki yi sallah. Umarni ne.”
Ta miƙe tana magana a hankali, ta shiga bayi.
Shi kuwa ya koma ɗakinsa domin ya duba ɗansa, Mahboob. Ya same shi yana bacci, ya kwanta kusa da shi yana shafa kansa, yana jin ƙaunar ɗansa na ƙaruwa a zuciyarsa, har bacci ya ɗauke shi.
Da safe misalin ƙarfe 8:00 na safe, aka kawo musu abinci. Amaryar tana bacci har wajen tara. Bayan ta tashi, ta yi wanka ta shirya cikin doguwar riga ja, ta ɗaura farin gyale a salo irin na Aisha Buhari.
Ta nufi ɗakin Ashraf, amma ba ta same shi ba. Ta shiga parlour, a kan dining ta same shi yana ciyar da ɗansa farfesun kaza.
Ranta ya ɓaci matuƙa, amma ta ɓoye hakan. Ta ƙarasa da murmushi ta ce:
“Good morning honey.”
Bai ko kalle ta ba, ya ce a taƙaice:
“Morning.”
Ta ja kujera ta zauna. Mahboob ya kalle ta ya ce:
“Who are you?”
Ta yi murmushi ta ce:
“I’m your new mom. Good morning son.”
Yaron ya haɗe fuska ya ce:
“No! You are not my mum and you will never be.”
Haushi ya kama ta sosai, amma ta danne, ta ɓoye a zuciyarta tana shirin abin da za ta yi idan mahaifinsa ya fita.
Ashraf ya juyo ya kalli Mahboob, ya ce:
“My lovely son, try to accept her as your new mom.”
Yaron ya girgiza kai yana kuka:
“No daddy, I don’t like her. Please take me to my real mom.”
Hannu ya ɗora a bayansa yana lallashi:
“Shhh… stop crying my boy. I promise you, zan nemo maka ita, kuma zan aure ta. Ka daina kuka.”
Mahboob ya ɗago kai, ya miƙa hannu yana cewa:
“Dad, promise?”
Murmushi ya yi masa ya ce:
“Promise, my little son.”
Nan take Mahboob ya rungume shi, ya zauna a cinyarsa yana ci gaba da cin abincinsa.
Da ya ɗan juyo, sai suka haɗa ido da amaryar mahaifinsa, ya sakar mata gwalo.
A zuciyarta kuwa ta ce:
“Zaka ci uwar ka ne yaro… zan gyara maka zama.”
Sai ta ja kular farfesun kaza ita ma ta fara ci.
*****
A ɓangaren Binafa kuwa…
Jikin umminta ya samu sauƙi sosai. Tana iya tashi da kanta, ta yi wanka da kanta, har sallah tana yi. Sai dai magana ce kawai ba ta dawo ba.
Kullum Binafa tana yi mata addu’a, tana bata ta sha, har ma tana shafa mata a jikinta.
Duk da haka, har yanzu tana neman hanyar tserewa daga gidan Daddy, amma bata samu ba.
A wani lokaci da Daddy ya zo ya duba su, sai ta ji yana waya. A nan ne ta fahimci cewa ya shiga siyasa—yana neman kujerar gwamna.
Wata rana tana zaune, kanta a kan cinyar umminta, sai wata dabara ta fado mata.
Da sauri ta miƙe ta fara buɗe drawers ɗin ɗakin, amma bata ga abin da take nema ba. Ta tsaya tana tunani, sannan ta leka ƙarƙashin gado.
A nan ne ta samu abin da take nema—wata doguwar igiya mai kauri.
Jikinta na rawa, ta ɗauki igiyar ta je jikin window, ta ɗaure ta sosai. Ta dawo ta gaya wa umminta cewa ta samu hanyar tsira.
Nan take ummi ta miƙe. Ita ce ta fara riƙe igiyar ta sauka a hankali.
Binafa ta biyo bayanta…
Da suka sauko ƙasa—
mai gadi ya buɗe gate… hancin mota ya bayyana a ƙofar.
