Skip to content
Hausa Novel

Hausa Novel

My WordPress Blog

  • Batsa Zalla
  • hausa novels
  • Toggle search form

ANYA UBANA NE

Posted on April 4, 2026April 4, 2026 By Maiallura No Comments on ANYA UBANA NE

ANYA UBANA NE
PAGE 4
Daga: Hausa Novel Dot Com
Littafin: ZULFA’U SA’EED IBRAHIM

Nan da nan idanun Ashraf suka kaɗa suka yi jazur, ran maza ya ɓaci, sai huci yake yi kamar wani zaki. Damƙo wuyan Binafa yayi ya haɗata da bango. Binafa, da taji hannun maza a wuyanta, nan da nan idanunta suka firfito, suka soma kawo ƙwallah har ta fara danasanin zuba masa jus ɗin da tayi a jikinsa.
Abbas ne da wasu mazan dake wajen suka ƙwace hannun Ashraf daga wuyan Binafa da ƙyar. Yana sakin wuyanta, ta koma gefe ta tsugunna tana mai da numfashin wahala.
A fusace Ashraf ya fita daga hall ɗin ba tare da ya kalli inda Abbas ɗin yake ba. Mota ya faɗa ya figeta a guje. Taimakon Allah ne ya kawo shi gida, ta ƙofar baya ya shiga ciki, saboda yasan idan ya shiga iyayensa suna nan zaune a parlour kuma sai sun cika shi da tambayar ina ya je ya ɓata kayan nasa da lemu. Gashi shi kuma kwata-kwata bai iya ƙarya ba, kuma abin kunya ne a gare shi ya faɗi gaskiyar abin da ya faru a gaban iyayensa.
Ɗakinsa ya shiga kai tsaye. Toilet ya yi ya cire kayan jikinsa yayi cilli da su, domin yadda yake jin tsanar Binafa haka yake jin tsanar kayan da ke jikinsa. Sakarwa kansa ruwa yayi, yafi ƙarfin minti 20 yana wanke jikinsa. Bayan ya fito ne ya zura kayan barcinsa sannan yayi addu’a ya kwanta. Amma kwata-kwata barci ya ƙi zuwa, abin da ya faru ne kawai yake dawowa masa a kwakwalwarsa.
Miƙewa yayi ya zauna, tabbas sai ya ɗauki mummunan mataki a kan wannan yarinyar, don shi bai taɓa ganin halittar da ya tsana a duniya sama da ita ba. Dogon tsaki yayi sannan ya kwanta ya rufe idanunsa.
A guje ta faɗa ɗakinta ta saki wani kuka mai ciwo. Idanunta jajir, zuciyarta sai tafasa take yi. Wallahi lazim bazata haƙura ba, abin da take ayyanawa a ranta kenan. Sai ta nuna wa wannan banzan mutumin shi ƙaramin ɗan iska ne da har zai mata wannan abin a cikin jama’a.
Wani ɓangare na zuciyarta ya ce mata, “duk ke kika ja komai ai.”
“Noooooo, ko ni na ja shi bai san darajar mace ba!” wani ɓangaren zuciyarta ya sake faɗa mata haka.
Lallai ne dole sai ta ɗau fansa akan abin da ya aikata mata. Sai ta rama—ramuwa mafi muni kuwa. Da wannan tunanin har barci ya ɗauke ta.
________________________________________
Da safe misalin ƙarfe 9:00am ta sauko ta fito domin wani fitinannen yunwar da taji tana addabarta. Kitchen ta nufa, ta soya indomie tare da haɗa tea, ta dawo dining ta zauna tana ci. Gadan-gadan har ta ƙoshi, ta kwashe kayan ta mayar da su kitchen.
Sama ta hau ta nufi ɗakin mahaifinta. As usual, sautin waƙar Olamide Oya WO ke fita daga ɗakin. Murmushi tayi ta ƙarasa ta shiga.
Zaune yake a kan kujera 1 sitter yana zukar sigari yana kuma karkada kansa, duka biyun (waƙar da sigarin) suna masa yawo a saman kansa tare da saka shi cikin nishaɗi.
Zama tayi a hannun kujerar tare da ɗaukar remote ta rage volume ɗin. A hankali ya ɗago ya kalle ta tare da faɗin, “Baby, har kin tashi?”
Gyada masa kai tayi. Kashe sigarin yayi ya fuskanceta, sannan ya ce:
“Binafa, nasan kina ƙoƙari sosai a wannan harka da na ɗora ki, kuma ina jinjinawa miki ƙwarai da gaske.”
Binafa na jin haka tayi murmushi, tasan wani abu ne yake son faɗa mata game da harkarsu.
“Ina fatan har yanzu baki manta da sharadin da na gindaya miki na banda soyayya ba?”
Dagowa tayi ta kalle shi tace, “ƙwarai kuwa Abba, nasan da wannan sharadi, kuma har yanzu bana kula kowa. Babu ma wani namiji a cikin raina. Ka kwantar da hankalinka Abba na.”
“Shi yasa a koda yaushe nake ƙara alfahari dake. Idan lokacin hakan yayi zan sanar dake.”
Binafa tace, “kada ka damu Abba na, faɗi matsayarka ta biyu, ko kuwa shi kenan?”
Abba ya girgiza kai yace, “akwai wata. Lokaci yayi da zaki rama min abin da Honourable Shitu ya aikata min. So nake ki je makarantar da autan jikansa yake, ki yi min kidnapping ɗinsa. Kada a fito da shi har sai ya bada million hamsin, tare kuma da azabtar da jikan nasa.”
Kuna sauraron littafin: ANYA UBANANE
Daga: Hausa Novel Dot Com
Kada ku manta ku yi:
Follow
Like
Share
Mun gode.

An gama Abba na, idan dai wannan ne, ka kunna TV anjima zaka ji a labaru an ɗauke jikan Honourable Shitu.”
“Na yadda dake ‘yata, ki je zaki samu sa’a.”
________________________________________
Mota ce ƙirar Range Rover baƙa wuluk, ta sha tinted. A gaba driver, a baya kuma wani kyakkyawan yaro da ba zai wuce shekara biyar ba yana shan ice cream, sai zubawa driver surutu yake yi, shima kuma yana biye masa.
Yaron kyakkyawa ne, fari tas, ga dimple. Leben nan nasa kalar pink, zaka rantse da Allah saka masa zan baki akayi. Gashin kansa baƙi sidik, wanda aka gyara masa ya kwanta a wuyansa.
Wani wawan birki naga driver ya taka yana salati. Wasu maza ne fuskokinsu rufe suka taso da bindiga, ɗaya kuma ya buɗe gidan baya ya ɗauko wannan yaron ya jefashi a mota, sannan suka jawo driver suka masa mugun duka, sannan suka ja motarsu a guje suka bar wajen.
________________________________________
A ruɗe driver ya tashi yana salati, domin yasan tashin ta kare idan, da wani baki zai iya faɗawa mai gidan sa wannan mummunan labari. Uwa uba idan Abdulkareem ya ji wannan labari sai ya kusa kashe shi, dama gashi da baƙar zuciya.
Hankali a tashe ya ɗaga waya ya kira uban gidan nasa a waya.
________________________________________
________________________________________
Zaune suke a katon parlour su uku. A bangon ɗakin na kalla na hango hoton wani kyakkyawan yaro har kala biyar, wani ba shi kaɗai bane—su biyu ne da wani kyakkyawan saurayi dake zaune kusa da mahaifiyarsa a ɗakin.
Abinci suke ci. Da ka kalli fuskokin waɗannan bayin Allah, farin ciki ne mamaye a fuskarsu.
Wayar dattijon dake kama da wannan saurayin ce ta ɗauki ruri. Kabar ba zai ɗauki wayar ba kasancewar yana cin abinci, sai kuma ya dubi sunan da ya fito a screen ɗin wayar.
Da azama ya ɗauka ya ƙara a kunnensa. Abin da ya ji ne ya firgita shi. Bai san sanda ya miƙe tsaye ba tare da faɗin “WHAT!” da ƙarfi.
“Wasu sun ɗauke Mahboob sun tafi da shi?”
Ai a ruɗe saurayin nan da mahaifiyarsa suka miƙe. Ita kuwa mahaifiyar har jikinta rawa yake yi.
Shi kuwa saurayin bai jira komai ba, ya fita da gudu ya nufi motarsa. Mai gadi na ganin haka ya wangale masa get ya fice a 80.
Parking yayi dai-dai inda aka saci Mahboob. Driver ɗin ya gani sai kai wa da kawowa yake yi.
Bai yi wata-wata ba ya fito ya tsinke shi da mari, ya kuma daga hannu ya sake tsinke shi da wani marin. Yana ƙoƙarin ƙara masa, sai yaji an riƙe hannunsa.
A fusace ya juyo domin ya ga wanda ya yi masa katsalandan, sai yayi tozali da idanun mahaifinsa.
________________________________________
“Ba ka da hankali ne Abdulkareem? Ba ka ganin irin raunikan dake jikinsa ba ne da zaka hau shi da mari? Ko kuwa da gangan ya bari aka ɗauke Mahboob? Haba Abdul, ka riƙa rage wannan baƙar zuciyar taka.”
Duk da shi ma tsohon hankalinsa a tashe yake, amma yayi ƙoƙari wajen danne abin domin komai sai a hankali.
________________________________________
Driver ne ya musu bayanin duk abin da ya faru.
Dattijon ne ya wa Abdulkareem umarni da ya tafi da driver asibiti, shi kuma zai wuce police station ya kai report.
________________________________________
To masu karatu, mu dai je zuwa…
Sai mun haɗu a next page.
Ku tuna: Comment, Like, da kuma Share ɗin ku shi ke Sani! Jin karsashin yin saurin suburbuɗo muku wani page ɗin!

Pages: 1 2 3 4 5 6 7 8 9
Uncategorized

Post navigation

Previous Post: D’AN FAARI Complete
Next Post: Gindi

Related Posts

D’AN FAARI Complete Uncategorized
Gindi Uncategorized
Доступ к играм и бонусам Vavada через зеркало Uncategorized
Vavada casino Uncategorized
GIDAN UNCLE Complete Uncategorized

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Archives

  • April 2026
  • November 2023
  • October 2023

Categories

  • Batsa Zalla
  • Uncategorized

Recent Posts

  • Wayyo Dadi Batsa
  • Yadda ake shan gindi da nono
  • Cin Gindi
  • Wayyo Nono na Gindi na
  • Kalaman Motsa Sha’awa

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on GIDAN UNCLE Complete

Copyright © 2026 Hausa Novel.

Powered by PressBook Masonry Blogs

Powered by
...
►
Necessary cookies enable essential site features like secure log-ins and consent preference adjustments. They do not store personal data.
None
►
Functional cookies support features like content sharing on social media, collecting feedback, and enabling third-party tools.
None
►
Analytical cookies track visitor interactions, providing insights on metrics like visitor count, bounce rate, and traffic sources.
None
►
Advertisement cookies deliver personalized ads based on your previous visits and analyze the effectiveness of ad campaigns.
None
►
Unclassified cookies are cookies that we are in the process of classifying, together with the providers of individual cookies.
None
Powered by