
ANYA UBANA NE
PAGE 7
Daga: Hausa Novel Dot Com
Littafin: ZULFA’U SA’EED IBRAHIM
Amai take ta kwararawa kamar zata amayar da ‘yan hanjin cikinta. Binafa duk tabi ta rude sai sannu take mata. Gashi kwanan su biyar kenan Daddy bai zo ya duba su ba, balle ya basu abinci. Saboda tsananin kuka idanunta sun jeme.
Da ƙyar ta iya kai maman nata bayi ta gyara mata jiki, sannan ta mayar da ita kan gado, ta gyara wajen da ta bata da amai. Wani irin nishi ummin nata take yi kamar numfashinta zai fita.
Miƙewa Binafa tayi tana ta bubbuga ƙofar ɗakin da ƙarfi kamar zata karya ƙofar, tana faɗin:
“Don girman Allah Daddy, kazo ka buɗe ƙofar nan mu kai Ummi asibiti, zata mutu! Don girman Allah ka taimake ni!”
Tafi ƙarfin minti goma tana buga ƙofar amma babu alamar za’a zo a buɗe. Komawa tayi wajen Ummi nata, amma sai taga bata numfashi. Hannu ta ɗora a kai, ta rusa uban ihu tana faɗin:
“Shikenan ta mutu! Na shiga uku…”
Durƙushewa tayi tana kuka sosai. Turo ƙofa taga anyi daga dara-daran idanunta tayi ta sauke akan na Daddynta, ta watsa masa wani mugun kallo. Ta ce:
“To bakin azzalumi, ka kashe min Ummina ka huta! Kuma ka sani Allah bazai taba barinka ba. Yadda ka zalunce mu, sai Allah ya saka mana. Bazamu taba yafe maka ba, kuma sai Allah ya tona maka asiri, sai Allah ya wulakanta ka duniya da lahira!”
Dariyar mugunta ya saki, sannan ya finciko gashin kanta yayi wurgi da ita a ƙasa, ya taka mata ruwan ciki. Ya ce:
“Dan uwarki, ni kike zagi? Sai in kashe ki, in kashe banza yar iska kawai! Ke har gata kike dashi aka faɗa miki? Uwarki mahaukaciya ce mara galihu. Na tsince ta da ciki a titi, na kuma dauko ta na kawo ta gida har ta haife ki. Na raina ki domin in yi amfani da ke ki kawo min dukiya, kuma gashi na tara. To yanzu baki da wani amfani a gare ni. Zan iya kashe ki ba tare da asara ba. Amma bazan kashe ki yanzu ba, domin akwai wani guda daya da ya rage min inyi, kuma da na samu abin nan zan zo na kashe ki ke da uwarki!”
Yana faɗin hakan ya juya ya kalli ƙofar ɗakin tare da faɗin:
“Shigo doctor.”
Wani saurayi wanda bai wuce shekara 30 ba ya shigo dauke da wata jaka a hannunsa. Kai tsaye wajen Ummi yayi. Buɗe jakar nan yayi ya fiddo kayan aikinsa ya soma duba ta.
Cikin lokaci kaɗan Ummi ta farfado daga dogon suman da tayi. Ruwa ya dora mata sannan ya mata wasu ‘yan gwaje-gwaje. Ya maida kayan cikin jaka ya miƙe ya kalli Daddy ya ce:
“Zan koma asibiti. Idan result din ya fito zan sanar maka matsalar. Amma ga wasu magunguna nan a rika bata akan lokaci, sannan a tabbata ta ci abinci, kada a dunga barinta da yunwa.”
Jinjina kai Daddy yayi, sannan suka fita dukkan su tare da kulle ƙofar.
Bayan kamar minti goma Daddy ya dawo da electric da kayan abinci ya aje mata sannan ya fice.
Binafa ta ce:
“Dan iska kawai!”
Tare da share hawayen da suka gangaro mata daga idanunta. Tashi tayi ta koma wajen Ummin nata ta riƙe mata hannu da aka ƙara mata ruwa, tana tofa mata addu’a. Duk lokacin da ta tofa mata addu’a sai ta saki ajiyar zuciya.
Sai wajen ƙarfe 3:30am na dare ta farka. Dama Binafa bata yi bacci ba. Ta sauko daga kan gadon ta haɗa mata tea mai kauri ta bata a baki, domin bata iya riƙewa da hannunta ba.
Sai da Ummi ta shanye tea ɗin nan tas, zufa sai karyo mata yake yi. Binafa ta ce:
“Ummi, in ƙara miki tea ɗin?”
Girgiza mata kai tayi, abin da yayi matuƙar bata mamaki kenan. Komawa tayi ta kwanta. Binafa ta rufe ta tare da tofa mata addu’a, sannan ita ma ta kwanta.
Kuna sauraron littafin: ANYA UBANANE
Daga: Hausa Novel Dot Com
Kada ku manta ku yi:
Follow
Like
Share
Mun gode.
Bayan kwana biyu, Daddy suka ƙara dawowa da wannan doctor ɗin. Ya ƙara dubata sannan ya ƙara mata wasu magunguna, tare da ƙara jaddada musu a kula da abincinta domin ulcer ya mata mugun kamu sakamakon rashin abincin da bata ci.
Binafa kuwa ta dage wajen kula da umminta tare da bata magungunanta. Jikinta kuma Alhamdulillah ya soma samun ƙarfi, sannan duk maganar da Binafa ta mata, tana bata amsa da kai ko hannu, sai dai magana har yanzu bata yi.
________________________________________
Bangaren Abdulkareem Ashraf kuwa, yana nan yana ta neman aure. Ya samu wata yarinya wacce yake ganin za ta iya kula da Mahboob ɗinsa, kuma ba za ta wulakanta masa iyayensa ba. Ya je wajenta, kuma bai wani sha wahala ba ta amince masa. Lokacin da mahaifiyarsa ta ji labarin, ba ƙaramin daɗi ta ji ba. Ya kuma tura manyansa, aka sa biki nan da wata ɗaya.
A yau ne kuma aka ɗaura auren Abdulkareem Ashraf tare da matarsa Zaheeda Mukhtar akan sadaki naira dubu hamsin. An kai ta gidan da ta zauna, dan ƙarere mai, domin ba a kawo da komai ba—komai shi ya siya, kama daga furnitures zuwa kayan kitchen. Gaskiya gidan ya haɗu.
Rigima ake ta yi tsakanin Ashraf da mamansa. Ya dage sai ya tafi da Mahboob, ita kuma ta ce ya bari a ɗan kwana biyu sai ya tafi da shi. Shi kuma ya yi zamansa a parlour, yana cewa idan dai bai tafi da Mahboob ba, to shi ma babu inda zai je.
Saukowa tayi ta zo parlour domin ta ɗauki casbaha ɗinta. Mutum ta gani kwance a kan doguwar kujera har ya soma barci. Daga kai tayi ta kalli agogon parlour—karfe 11:30 na dare. Hannu ta sa ta soma tashe shi. Buɗe ido yayi ya sauke akanta.
Ta ce,
“Ka na hauka ne Ashraf? An sa maka mata a gida, amma har yanzu kana kwance anan kana barci?”
Ashraf ya ce,
“Ummi, na faɗa miki—idan dai ba da Mahboob ba, ni babu inda zan je. Ni fa saboda shi da kuma farin cikin ku na yi auren nan.”
Umminta ta ce,
“To na ji, tashi ka je ka ɗauke shi ku tafi.”
Aikuwa miƙewa yayi ya ɗauko Mahboob ya ɗora shi a kafada ya fice. Already dama ya faɗa wa Abbas baya son rakiya, tunda shi ba yaro ba ne.
Ko da ya dawo gida, kai tsaye ɗakinsa ya nufa. Ya kwantar da Mahboob, sannan ya shiga bayi ya watsa ruwa yayi alwala. Doguwar jallabiya ya saka ya nufi ɗakinta.
Zaune ya tarar da ita a bakin gado, wata fitinanniyar rigar bacci ne a jikinta—mai suna fan, darin ka tsirara. Kau da idanunsa yayi sannan ya mata umarni da ta shiga bayi ta yi alwala yana jiranta.
Miƙewa tayi tana karkada jikinta ta shige bayin. Shi kuma fita yayi domin ya manta da kazar da ya sayo a cikin mota. Sai da ya bi ta kitchen ya ɗauko plate.
Ko da ya dawo ɗakin, ta riga ta fito da jimawa. Umarnin ya mata da ta ɗaura zani ta saka hijjab su yi sallah. Bayan sun idar, ya dafa kanta ya karanta addu’ar da ake so kowane ango ya yi wa amaryarsa.
Kazan ya ɗauko ya aje a gabanta ya ce:
“Bismillah, amarya.”
Sai mun haɗu a next page.
Ku tuna: Comment, Like, da kuma Share ɗin ku shi ke Sani! Jin karsashin yin saurin suburbuɗo muku wani page ɗin!
