
ANYA UBANA NE
PAGE 5
Daga: Hausa Novel Dot Com
Littafin: ZULFA’U SA’EED IBRAHIM
An yi bincike sosai, amma ba a gano su waye suka ɗauke Mahboob ba. Hankalin Abdulkareem ya tashi matuƙa, domin yana matuƙar ƙaunar tilon ɗansa. Haka ma a wajen kakansa, addu’a kawai ake yi Allah ya bayyana inda yake.
________________________________________
A ɓangaren Binafa kuwa, da ta ga yaron sai ta ji wata irin ƙauna ta mamaye zuciyarta. Ta yi murmushi tana cewa:
“Zo, yaro na.”
Sai ya ja baya, ya murguda baki yace:
“Ni ba yaronki ba ne! Ki kai ni wajen grandpa da daddy na. Ni gida zan je!”
Nan take hawaye suka cika idanunsa.
Tausayinsa ya ratsa zuciyarta. Ta ƙarasa kusa da shi tana cewa:
“Ni ma mama ɗinka ce. Zan siya maka ice cream, mu kalli cartoon tare, sannan zan kai ka wajen daddy ɗinka.”
Sai ya yi murmushi, dimples ɗinsa suka bayyana, suka fito da ainahin kyawunsa. Ita kuma sai ta ji kamar ta taɓa ganin fuskar nan a wani wuri.
Mahboob yace:
“Da gaske kika ce zaki zama mummy na? Ni fa bani da mummy, sai daddy da grandpa da grandma. Idan kin kai ni gida, zan nuna ki ga daddy na, nace masa ke ce sabuwar mummy na.”
Hawaye masu zafi suka zubo daga idanunta. Ta rungume shi tana cewa:
“Ina ƙaunarki, yaro na.”
Shi ma ya ƙara rungumeta sosai yace:
“Ni ma sabuwar mummy, ina sonki sosai.”
A zuciyarta ta yanke shawara — ba za ta bari a cutar da wannan yaron ba. Duk wanda ya yi yunƙurin cutar da shi, a shirye take ta ɗauki mataki akansa.
________________________________________
Kwana ɗaya kawai Mahboob ya yi a wajen Binafa, amma sun yi wata irin shakuwa. Tare suke cin abinci, tare suke barci, har ma suna fita su buga ball tare.
Ta siya masa kaya masu tsada, tana jin kamar da hali zata riƙe shi har abada. Amma ta san hakan ba zai yiwu ba.
Domin yau ne za su kira kakansa su nemi kuɗin fansa. Ta san iyayensa ba talakawa ba ne — suna da kuɗi kuma suna matuƙar ƙaunar yaron.
________________________________________
Gardi ya kira Honourable Shitu ta waya, ya faɗa masa kuɗin da suke buƙata, tare da gargaɗi mai tsanani:
“Idan kuka zo da ‘yan sanda, sai dai ku karɓi gawar jikan ku.”
A firgice Honourable ya amince, yana cewa:
“Zan bi umarninku. Ba wanda zai sani. Ni kaɗai zan zo na karɓi jikana.”
Gardi ya faɗa masa inda zai ajiye kuɗin, inda zai karɓi yaron, da kuma lokacin.
________________________________________
Binafa kuwa sai ta ji kamar ta ɗauki Mahboob ta gudu da shi.
Ta zauna kusa da shi yana cin ice cream tace:
“Mahboob, yau zan kai ka gida.”
Sai ya ɗago ya kalleta yace:
“Sabuwar mummy, tare zamu tafi ko?”
Ta ce:
“A’a, zan sa a kai ka. Ni daga baya zan zo gidan ku.”
Sai ya rau-rau da ido, alamun zai yi kuka:
“Ni dai babu inda zan je sai dake!”
Ta yi murmushi tana ƙoƙarin kwantar masa da hankali:
“Ni ma yau zan zo gidan ku. Zan tsaya na yi mana sayayya — ice cream da ball — sannan in zo mu yi wasa.”
Sai ya ƙara ƙin yarda:
“A’a sabuwar mummy, ki bini kawai mu tafi tare. Daddy zai kai mu a mota.”
Shiru tayi, tana tunanin mafita. Sai wata dabara ta zo mata.
Ta ce:
“Mahboob, kana son allura?”
Nan take ya zaro ido:
“Ni bana son allura! Ko bana lafiya ma bana so. Daddy na ya sani. Idan yace zai kai ni allura, sai in gudu wajen grandma.”
Ta yi murmushi tace:
“To ni ma kaina na ciwo, sai na je asibiti ayi min allura. Idan ka nace sai tare zamu je, to mu je a yi mana tare.”
Nan take ya girgiza kai:
“A’a sabuwar mummy, ki je ke. Ni a kai ni gida. Idan kin dawo sai ki zo gidan mu.”
Ta yi murmushi a zuciyarta tace:
“Haka ne yaro na. Daga nan zan je na yi mana sayayya, har da ball, mu yi wasa.”
Sai ya yi tsalle ya rungumeta yace:
“Yauwa sabuwar mummy! Kuma harda grandpa da daddy zamu buga ball!”
Ta ce:
“Tabbas yaro na.”
Sannan tace:
“Yanzu tashi mu je mu dafa Indomie mu ci, sannan in maka wanka in saka maka kaya masu kyau.”
Kuna sauraron littafin: ANYA UBANANE
Daga: Hausa Novel Dot Com
Kada ku manta ku yi:
Follow
Like
Share
Mun gode.
A ɓangaren Honourable Shitu kuwa…
Bai faɗawa kowa yadda suka yi da masu garkuwa da Mahboob ba. Dalili kuwa, ya san halin ɗansa—mai zafi da muguwar zuciya—wanda zai iya nacewa sai an bi diddigin waɗanda suka sace ɗan nasa.
Amma kuma, masu garkuwar sun masa gargaɗi mai tsanani:
kar ya kuskura ya je da ‘yan sanda, domin idan ya yi haka… gawar yaron kawai za su ba shi.
Saboda haka ya shirya, da niyyar zai faɗa musu cewa zai koma police station, alhali a zuciyarsa yana ɓoye gaskiyar halin da ake ciki.
A lokacin, Hajiya Saudat na zaune akan darduma, tana ta kwararo addu’o’i cikin tsananin damuwa, tana roƙon Allah ya bayyana mata jikan nata a duk inda yake.
Sai da ta gama shafa addu’a sannan ya ce:
“Saudat… zan koma police station, in ji ko sun samu wani labari game da jikanmu.”
Hawaye suka gangaro daga idanunta, ta ce:
“To Allah ya sa a dace… Kaga Abban Mahboob kuwa? Na roƙe shi ya ci wani abu amma sam ya ƙi. Yace ba zai iya saka komai a bakinsa ba sai ɗansa ya bayyana.”
Ya tambaya cikin damuwa:
“To Abdulkareem ɗin yana ina yanzu?”
Ta girgiza kai:
“Ai tun safe da ya fita ban ƙara ganinsa ba har yanzu…”
Ya sauke ajiyar zuciya, ya ce:
“Ki kwantar da hankalinki… Insha Allah za a ga Mahboob.”
________________________________________
A gefe guda kuma…
Tsaye yake a inda Gardi ya umarce shi da ya tsaya. Su kuwa suna cikin wata mota mai nisa, suna kallonsa ba tare da ya sani ba.
Sai wayarsa ta yi ƙara.
Da sauri ya ɗaga.
Umarnin farko suka ba shi:
“Ka buɗe green ɗin motar da ke gabanka, ka saka kuɗin a ciki.”
Hannunsa na rawa, ya buɗe motarsa, ya ɗauko wata katuwar jaka, ya saka kuɗin a cikin motar kamar yadda aka umurce shi.
Sai suka sake cewa:
“Ka ƙarasa gaba… za ka ga wata mota kalar ash. Ka buɗe ta, za ka samu jikan ka a ciki.”
Zuciyarsa na bugawa da ƙarfi, ya ƙarasa da sauri.
Ya buɗe motar…
Sai ya ganshi—Mahboob.
Sanye da T-shirt purple, wando jeans baki, cap purple, da takalmin Timberland mai haɗa baki da purple. Yaron yayi kyau ƙwarai… sai dai fuskar sa a murtuke take.
Da ya ɗago idonsa ya haɗu da na kakansa—
Nan take ya miƙe ya rungume shi da ƙarfi, cikin farin cikin ganinsa.
Kakansa kuwa ya ɗauke shi ya matse a jikinsa, zuciyarsa cike da godiya ga Allah.
Ba tare da ɓata lokaci ba, ya kai shi mota, ya zaunar da shi a gaba, sannan ya zagaya ya zauna a kujerar driver, ya ja motar suka wuce.
________________________________________
A nesa kaɗan…
Binafa na kallon duk abin da ke faruwa daga cikin wata baƙar mota mai tinted.
Hawaye suka zubo mata ba tare da ta sani ba.
Ta ji kamar ta fito ta roƙe su su bar mata Mahboob… amma ta san hakan ba zai yiwu ba.
Gardi ya zo ya buɗe motar da aka ajiye kuɗin, ya ɗauko su, ya taho inda take, ya ajiye a bayan motarta, yana cewa:
“Boss… ga kuɗin nan.”
Ta ce a sanyaye:
“Cire million ashirin ku raba.”
Nan take ya cire kuɗin, ya saka a wata jaka, ya rufe motar ya wuce.
Ita ma ta tada motarta ta wuce gida…
Binafa na shiga ɗakin mahaifinta, sai ta ji waya tana ƙara.
“To ni hauka nake yi?” muryar mahaifinta ta faɗo daga wayar.
Sai ta nufi wajan ɗan TSITO, aka… amma kafin ta fahimci komai, mahaifinta ya ɗago ya haɗu da idonta. Murmushi ya sakar mata, ya yi sallama da wanda yake wayar da shi, ba tare da ya kammala abunda yake faɗa ba.
Binafa kuwa, mamaki ya lullube ta. A yau bata ji wakar safe na mahaifinta a ɗakin ba kamar yadda ya saba. Ta zauna a kujerar ɗaya, ta ce:
“Wash… na gaji wallahi, daddy.”
Idanunta sun sauka zuwa wancan kofofin ɗakin wanda bata taɓa lura da shi ba sai yau. Ta ce:
“Daddy, ban taɓa lura da wancan ɗakin ba, bari na shiga na gani.”
Mikewa tayi, zata tafi, sai wani razan tsawa ya ɗaka mata, har ‘ya’yan hanjinta suka ƙara tsotse.
Muryar mahaifinta ta yi ƙarfi, har ta fita daga bakin sa:
“Wallahi, duk ranar da kikayi gigin shiga wancan ɗakin, sai na illataki, sai na muzantaki, kuma ƙarshen ki ne yazo a wannan duniya…”
Tsoro ya lullube ta gaba ɗaya. Ido ta riƙe na mahaifinta da tsoro da mamaki.
Ahankali ta furta:
“Dadi… kai ka haife ni kuwa?”
Wani abu ya ɗaga a tsakiyar zuciyar mahaifinta, kamar an buge masa guduma. Nan da nan ya dawo cikin nutsuwa, ya ce…
Tooofah, masu karatu!
Kun ji fa? Me yasa mahaifin Binafa ya haramta mata shiga wannan ɗakin?
Meyasa kuma ya furta waɗannan kalmomi masu tsanani a kanta?
Duk sai kun biyo ni a hankali, zan warware muku wannan kullin… kuma gaskiya zata bayyana ɗaya bayan ɗaya.
Sai mun haɗu a next page.
Ku tuna: Comment, Like, da kuma Share ɗin ku shi ke Sani! Jin karsashin yin saurin suburbuɗo muku wani page ɗin!
