Skip to content
Hausa Novel

Hausa Novel

My WordPress Blog

  • Batsa Zalla
  • hausa novels
  • Toggle search form

ANYA UBANA NE

Posted on April 4, 2026April 4, 2026 By Maiallura No Comments on ANYA UBANA NE

ANYA UBANA NE
PAGE 2
Daga: Hausa Novel Dot Com
Littafin: ZULFA’U SA’EED IBRAHIM
Miƙewa suka yi suka shiga mota, da gudu wasu maza guda uku suka zo wajen motar nan ta tsakiya wadda Binafa ta hankaɗa dattijon nan a ciki. Tambayarsa suka fara yi ko da akwai wani waje da yake masa ciwo, girgiza musu kai kawai ya yi, sannan ya musu nuni da su wuce.
A hanya babu abin da ke wa wannan dattijon ƙunci illa matashiyar yarinyar nan da ta wulakanta rayuwarta ta zo tana fashi a titi. Babu abin da ya dace da ita illa aure. Hawaye ne suka gangaro masa, ya yi saurin gogewa da tafin hannunsa. Ba wai kuɗinsa da suka tafi da su ba ne ya daga masa hankali ba, illa yadda yarinya ƙarama ta wulakanta kanta.
Million biyar ta cire ta ba su gardi su raba. “THANK YOU BOSS” abin da suka ce mata kenan, sannan suka saka mata kuɗin a bayan mota. Shiga ta yi cikin motar, dai-dai nan aka kwala kiran assalatu. A 80 ta figi motar, ko da ta iso gida an riga an idar da sallar asuba. Ko ta kan daddyn ta bata yi ba, duk da ta san yana can yana barci tunda shi sallah bata dameshi ba.
Gudu-gudu ta watsa ruwa, ta saka doguwar riga ta tada sallah. Bayan ta idar ta ɗauko Alƙur’ani ta soma karantawa. Bayan ta gama ta daɗe tana addu’a sannan ta shafa, ta bi layin gado sai barci.
Ba ita ta tashi ba sai ƙarfe sha biyu da rabi, nan ma ba ta fito ba sai da ta jira aka yi kiran sallar azahar sannan ta yi. Fitowa ta yi ta shiga kitchen, irish ta soya tare da miyan ƙwai sannan ta haɗa tea mai kauri, ta zo ta jera a dining table. A hankali take ci har ta gama, sannan ta kwashe kayan ta kai su kitchen.
Hanyar corridon da zai sada ta da palon daddyn ta ta bi, as she expected, kiɗa ne ke tashi na waƙar lilwayne (MIRROW). Yana zaune akan kujera, ƙananan kaya ne a jikinsa amma wandon da kaɗan ya wuce gwiwarsa, wannan karon sigari yake sha.
“Morning dad.”
“Morning my daughter,” ya amsa mata tare da kashe sauran sigarin ya ajiye akan faranti.
“Ina fatan an yi nasara?” ya tambaye ta.
Murmushi ta yi masa, shi kuwa ya wage bakinsa ya saki dariya, “hahahaha kamar an tashi injin markaɗe domin na san murmushinki na nuna alamun nasara ne. Million 15 ne, na sallami su gardi da million 5, sauran suna cikin mota.”
Daddy ya ce, “Shi yasa a kullum nake ƙara jinjina miki domin ke din jini na ce. Na san nan gaba sai ki ce ban yi komai ba. Na san barewa ba ta gudu ɗanta ya yi rarrafe. Ina alfahari da ke.”
Binafa ta ce, “Daddy ka da ka damu, domin ni sai na saka Ummi na nadamar abin da ta maka. Shi yasa kwata-kwata bana kaunar ta, tun da har ta iya barina tun ina da ƙwa uku a duniya, a dai-dai lokacin da na fi buƙatar ta, ta yar da ni, ta kuma gujeni, ba ta kuma waiwaya ta ba, don kawai Allah ya yi ka talaka.”
Tana kaiwa nan ta fashe da matsanancin kuka. Shafa kanta ya soma yi, “Ki yi shuru baby na, ba gashi ta sanadiyar ki na tara abin duniya ba? Me za ki nema ki rasa a duniyar nan yanzu?”
Binafa ta ce, “Yanzu Daddy, tun da Ummi ta ajeni ta gudu bata ƙara waiwaya ta ba?”
Kuna sauraron littafin: ANYA UBANANE
Daga: Hausa Novel Dot Com
Kada ku manta ku yi:
Follow
Like
Share
Mun gode.

Ɗan guntun hawaye ya share ya ce, “Har kauyan su na bita, aka ce sun bar kauyan ma gaba ɗaya. Ranar da zata gudu, har durkusawa nayi ina bata hakuri tace ita sam ba zata iya zama da talaka ba, kuma babu inda zata tafi dake, kuma sai na sake ta, domin taje ta auri mai kuɗi. Kasancewar mahaifiyar ki mai kyau ce, ita kika biyo a kyawu. Haka nan, ba da son rai na ba, na rubuta mata saki ɗaya, tako ajiye min ke tayi tafiyar ta. Tun daga lokacin, ban kuma ganinta ba har yanzu.”
Kukan Binafa ya tsananta, ta tashi da gudu, tayi ɗakin ta, tana ƙara jin tsanar ummin nata a ranta.
Doguwar bakar jallabiya ce a jikinta, mai ƙwalliyar duwatsu kalar ja har ƙasa, sai tayi rolling kanta da bakin mayafin jallabiyar. Duk da ba wata ƙwalliya tayi ba, amma tayi matuƙar kyau. Driving take yi amma ranta a cunkushe yake, tama rasa inda zata je. Can dai tayi hanyar park, tana isa tayi parking, ta fito ta sami gujera da babu kowa a wajen ta zauna, cus she one to be alone. Ice cream kawai ta siya, ta zauna tana sha kadan-kadan.
Wasu samari ne guda biyu, nesa da ita kaɗan, suma suna shan ice cream. Dayan ne ya fara hango ta, ya dan zunguri, dan uwansa ya ce, “Ashraf, ga type ɗinka can, wallahi yarinyar tayi.”
Wanda aka kira da Ashraf ko kallon wajen bai yi ba illa wani dogon tsaki da ya ja, ya ce, “Mai meyasa kai Abbas, babu abin da ka saka a gaba sai mata ne? To ni ba haka nake ba, idan kaga kai zaka iya ka je, amma ni babu inda zan je.”
Abbas ya ce, “Kai inaah, wannan tafi ƙarfi, na dai dai da kai ne, da zaka duba ko sau ɗaya ne nasan zaka faɗa.”
Dogon tsaki ya ja, ya mike tare da ɗaukar key ɗinsa, ya ce, “Sai ka tawo, don ni na wuce, ba zan iya da iskancin ka ba.”
Ko kallon inda take bai yi ba, ya wuce wajen motar shi yayi mata key. Abbas na ƙwalla mishi kira, ko kula sa bai yi ba, ya wuce. Girgiza kansa yayi, domin shi abu mai mamaki yake bashi, shi kwata-kwata bai ganewa abokin nashi ba. Shi sam yan mata ba sa gaban shi, wani lokacin sai ya ga kamar abokin nashi ba shi da lafiya ne.
Driving take yi amma kwata-kwata hankalinta baya jikin ta. Ta je park ne domin ko zata samu damuwar ya ɗan ragu, amma sam sai ta ji ƙaruwa ma yayi.
Da gudu ta danno motar, yayi iya bakin ƙoƙarin sa ya kauce mata, amma duk da haka sai da ta bugan masa mota, kuma tana ciki ba ta fito ba, balle yayi tunanin zata bashi hakuri. Yaƙi matsawa, itama taki matsawa, ga shi sun haɗa goslow. Haushi kamar ya kashe shi, yaji tsanar ta ya darsu cikin ransa. Ita kuwa tsoro ne ya hanata fitowa, duk da tana rike bindiga ta yatsa a gaban maza. Amma wannan ba ƙaramin ƙwarjini ya mata ba, sai da yaga mutane suna fitowa suna kwankwasa masa glass, wasu na zagin su, wasu na masifa. Sannan yayi gaba da motar, dai-dai saitin ta ya sauke glass, ya ce, “Wawuya da kikiya, jaka kawai,” sannan ya cilla motar shi yayi gaba.
Zagin da ya mata yayi matuƙar bata mata rai, domin sai da hawaye ya zubo mata. Ta kuma ɗauki aniyar duk inda ta kara ganin shi sai ta masa rashin mutuncin da bai taba ganin irin sa ba.
Muje zuwa

✍🏼

Sai mun haɗu a next page.
Ku tuna: Comment, Like, da kuma Share ɗin ku shi ke Sani! Jin karsashin yin saurin suburbuɗo muku wani

Pages: 1 2 3 4 5 6 7 8 9
Uncategorized

Post navigation

Previous Post: D’AN FAARI Complete
Next Post: Gindi

Related Posts

GIDAN UNCLE Complete Uncategorized
Доступ к играм и бонусам Vavada через зеркало Uncategorized
D’AN FAARI Complete Uncategorized
Vavada casino Uncategorized
Gindi Uncategorized

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Archives

  • April 2026
  • November 2023
  • October 2023

Categories

  • Batsa Zalla
  • Uncategorized

Recent Posts

  • Wayyo Dadi Batsa
  • Yadda ake shan gindi da nono
  • Cin Gindi
  • Wayyo Nono na Gindi na
  • Kalaman Motsa Sha’awa

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on GIDAN UNCLE Complete

Copyright © 2026 Hausa Novel.

Powered by PressBook Masonry Blogs

Powered by
...
►
Necessary cookies enable essential site features like secure log-ins and consent preference adjustments. They do not store personal data.
None
►
Functional cookies support features like content sharing on social media, collecting feedback, and enabling third-party tools.
None
►
Analytical cookies track visitor interactions, providing insights on metrics like visitor count, bounce rate, and traffic sources.
None
►
Advertisement cookies deliver personalized ads based on your previous visits and analyze the effectiveness of ad campaigns.
None
►
Unclassified cookies are cookies that we are in the process of classifying, together with the providers of individual cookies.
None
Powered by