ANYA UBANA NE
PAGE 1
Daga: Hausa Novel Dot Com
Littafin: ZULFA’U SA’EED IBRAHIM

*بسم الله الرحمن الرحيم*
Gida ne tankameme, an yi masa fenti kalar lemon green da fari. Kai tsaye idan ka kalli gidan, zaka gane cewa kuɗi sun yi kuka a cikinsa, domin gaskiya bakina ba zai iya fasalta muku tsarinsa yadda ya kamata ba.
Ban kai ga rikicewa ba sai da na kutsa cikin gidan—nan take numfashina ya kusa ɗaukewa. Motoci na gani kala-kala, sun kai kusan goma sha biyu a parke a waje, kuma duk ba kanana ba ne, na alfarma ne.
Shiga nayi cikin falon…

aljannar duniya kenan! Komai na cikin falon sky blue ne, daga kujeru zuwa labule da kayan ado.
Na bi wani corridor, kawai sai na tsinci kaina a cikin wani ɗaki wanda komai na cikinsa pink da purple ne—daga gadon da labule har zuwa wardrobe.
Sai na ji ƙarar ruwa daga bathroom, hakan ya nuna min mai ɗakin tana ciki. Bayan kamar mintuna goma, sai gata ta fito ɗaure da towel wanda ya dan wuce cinyarta kaɗan, tana goge kanta.
Wata doguwar, kyakkyawar budurwa ce—jikinta santsi kamar an shafe shi da mai, fara tas mai kyau da shape irin figure 8. Tana da manyan idanu masu ɗaukar hankali, ga dogon hanci da ya ƙara fito da kyawun fuskarta. Bakin ta madaidaici ne, mai ɗauke da launin pink kamar ta shafa jan baki.
Ta je gaban madubi ta baza gashinta wanda ya sauko har kafadunta. Ta ɗauko hand dryer ta fara busar da gashin. Ashe ba nan ba ne ƙarshen abin mamaki—gashin har tsakiyar bayanta ya sauko, baki sidik mai kyau.
Sai ta ɗauko mai ta shafa a jikinta, sannan ta ɗauko turare ta fesa jikinta da kamshi.
Ta saka bra fari, sannan ta ɗauko bomb short kalar blue-black ta saka. Ta ƙara da wata ƙaramin half vest kalar pink, sannan ta ɗauko wata doguwar riga mai ɗan bayyana jiki kalar pink ta saka.
Ta gyara gashinta da kyau, ta tara shi a tsakiyar kanta, sannan ta ɗauko wani ƙaramin veil kalar pink ta ɗaura, gashin nata yana fitowa da kyau.
Masha Allah… Allah ya yi halitta sosai a wajenta.
Ta sake fesa turare, sannan ta ɗauko wata jaka kalar blue-black mai siririn hannu, ta saka wayoyinta a ciki. Ta buɗe drawer ta ɗauko bandir na kuɗi (₦1000), ta saka a jaka tare da car key.
Daga nan ta nufi wajen takalmanta, ta ɗauko wani blue-black mai tsini ta saka, sannan ta fito zuwa falon.
Ta bi wata hanya da ta haɗa da matakala, ta hau sama. Tun kafin ta isa falon, sai ta ji wakar Bob Marley tana tashi a hankali.
Wani katon falo ne a sama—komai na cikinsa golden da silver ne. A kan kujera 2-seater kuwa, wani babban mutum ne zaune, fuskar sa sanye da glass na alfarma, ya miƙe hannunsa yana riƙe da jarida yana karantawa cikin nutsuwa.
Kuna sauraron littafin: ANYA UBANANE
Daga: Hausa Novel Dot Com
Kada ku manta ku yi:
Follow
Like
Share
Mun gode.
Ta ƙarasa wajen home theater ta rage ƙarar waƙar. Da ya ɗago ya kalle ta, sai ya saki murmushi tare da cewa:
“Baby, har kin fito?”
Ita ma murmushi ta mayar masa, ta ƙarasa wajensa ta bashi peck a goshi sannan ta ce:
“Yes Daddy, har na shirya zan tafi. A can zan kwana domin akwai operation ɗin da za mu yi da su gardi around 2:30. Kaga yanzu it’s almost 1:30, I have to hurry.”
Ya riƙo hannunta ya sumbace shi, sannan ya ce:
“Ina alfahari da ke, Binafa. Lallai ke jini na ce. Ki tabbata yau kin kawar da Alhaji Mahmud daga doron ƙasa. Ina so da safe in ji labarin baya raye.”
Da sauri ta ɗago ta kalle shi, tana girgiza kai:
“No Daddy, noooo! Ba zan iya kashe mutum ba. Kai ne ka saka ni cikin wannan, amma ba zan bari a kashe mutum a gabana ba. Zan dai karɓo maka kuɗin da kake so, amma kisa kam ba zan yi ba.”
Ya murtuke fuska yana cewa:
“Haba Baby, me yasa baki son ki yi kisa?”
Ta ce:
“Dad, laifin kisa babba ne. Duk da shi ma fashi babban laifi ne, amma gwara na ɗauki wannan. Kisa kam ba zan iya aikatawa ba, sam.”
Sai kawai ya ɗaga hannu alamar ta tafi. Tana kaiwa ƙofa, sai ya daga murya ya ce:
“GOOD LUCK.”
________________________________________
2:30 AM
Motoci guda biyar ne suke tafiya a jere, amma wacce ke tsakiya ita ce mafi tsada. A cikinta akwai wani dattijo tare da direbansa. Kyakkyawa ne, fari tas, wanda idan ka gan shi zaka san a lokacin ƙuruciyarsa ya ɗauki hankalin mata sosai.
Ba su jima ba sai suka hango wasu gardi a tsakiyar hanya, dauke da bindigogi, fuskokinsu a rufe.
Nan take motocin suka tsaya cak, ana ta karanta Inna lillahi…
Gardi suka ruga wajen motocin, suna fito da mutanen ciki da ƙarfi. Sai da suka fitar da su gaba ɗaya, har da dattijon nan, sannan suka umarce su da su kwanta a ƙasa.
A daidai wannan lokacin, sai aka ji wani tsawa—sai ga Binafa ta fito. Tana sanye da doguwar riga baƙa mai zip daga sama har ƙasa, fuskar ta a buɗe, bindiga a hannunta.
Ta ƙarasa kusa da dattijon, ta ɗora bindigar a kansa tana cewa da ƙarfi:
“Tashi na ce!”
Da rawar jiki ya miƙe. Ta ja shi har kusa da motarsa, sannan ta ce:
“Fiddo da duk kuɗin da ke cikin motar nan… ko yanzu ka bankwana da duniya.”
Jikinsa na rawa ya buɗe mota, ya fiddo wata katuwar jaka—mai ɗauke da kuɗi har miliyan goma sha biyar. Da ƙyar ya ajiye a gabanta.
Ta yi alama ga gardi:
“Ku zo ku ɗauka.”
Da sauri suka iso, suka kwashe kuɗin suka nufi cikin daji.
Ita kuma, ta tura dattijon cikin motarsa, sannan ta juya da gudu ta bi su cikin dajin—sauri kamar ba mace ba.
________________________________________

Tofa! Labari ya fara ɗaukar zafi…
• Shin Binafa zata iya tserewa daga wannan rayuwa?
• Ko kuwa zata shiga cikin mafi muni fiye da wannan?
Sai mun haɗu a next page.
Ku tuna: Comment, Like, da kuma Share ɗin ku shi ke Sani! Jin karsashin yin saurin suburbuɗo muku wani page ɗin!
