D’AN FAARI
PAGE 3
Daga: Hausa Novel Dot Com

Rungumo shi tayi a jikinta ta soma b’anb’aro kwarkwasar da suka manne a jikinsa suna ganna masa cizo. Yana hawaye ita ma ta na yi.
Sai da ta cire tas sannan ta kwantar da shi. Ta mik’e ta koma d’akinta ta d’auko man zafi ta dawo ta mulke masa bayan, sai ajiyar zuciya yake yi.
“Yi hak’uri ka ji Ahmadu, akwai Allah! Amma tabbas mahaifiyar ka bata da hankali gaskiya.”
Ta fad’i hakane tare da soma d’ibar abincin tana ba shi a baki. Sai da ya cinye tsaf sannan ta koma d’aki ta d’auko matashin mai ta saka masa, ta kuma gyara masa kwanciya sannan ta koma d’akinta. Taci nata abincin sannan ta shiga k’ulle-k’ullen sana’ar ta.
Inna Laadi kuwa ko sau d’aya bata tab’a gigin lek’owa ba, balle ta duba halin da Ahmad d’in ke ciki.
Abubakar k’anin sa, da ya ganshi hannu a d’aure, da gudu ya shiga d’aki yana fad’in:
“Innar mu! Innar mu!! Zo ki ga hannu Ahmadu an nannad’e da bandeji, karye wa yayi?”
Hannu ta saka ta bugan masa baki tare da fad’in:
“Ba na hana ku yi min maganar wannan yaron ba? Idan ka sake sai na fasa maka bakin ka, ka ji ni?”
Hannu Abubakar ya saka ya kama bakin tare da soma kuka yana fad’in:
“To Inna ai shima d’an ki ne kamar mu ko?”
Hannun sa ta kama duka biyun tare da zare masa idanu tana fad’in:
“Kar in k’ara ji! Shi ba d’ana bane! D’an rik’o ne?”
Shuru yaron yayi. Can kuma ya ce:
“Inna menene d’an rik’o?”
Tura shi tayi tare da fad’in:
“Kai tafin can! Bani son shegen surutu. Fita kayi wasa a waje.”
Fitowa Abubakar ya yi tare da zama kusa da Ahmad d’in da ke kwance. Ya kalle shi tare da fad’in:
“Ahmadu, wai Innar mu ta ce ba ita bace ta haife ka wai kai d’an rik’o ne. Da gaske ne?”
Inna Abu dake kwar d’aki tana bawa wata yarinya k’ullin kuka da tazo saya sai tayi caraf tace:
“Inji uban wa ya fad’a maka haka? To duk wanda ya fad’a maka ba Innar ku bace ta haife sa k’asurgumin mak’aryaci ne! Ahmadu bai da uwar da ta wuce Laadi. Uwar ku d’aya, uban ku d’aya da shi Ahmadu.”
Da sauri Abubakar ya shige d’aki, don sam basu shiri da Inna Abu. Make su take yi tana kiran su da y’ay’an so, sai tana huce haushin Inna Laadin a kan su.
Shi kuwa Ahmad bai ce komai ba. Ya mayar da kai ya kwanta.
Sai da Ahmad yayi wata guda cur da hannu a d’aure kana Inna ta koma da shi wajen wanzan ya kwance hannu, kuma alhamdulillah gyara yayi kyau.
Duk wannan zama da Ahmad yayi da ciwo ko sau d’aya Inna bata tab’a tambayan shi ya jiki ba ko kuma irin ta d’an nuna concern d’in nan. Idan kuwa suka had’u da mak’ota a waje aka tambaye ta jikin Ahmad d’in, ko kallon inda mutum yake ba ta kuma yi take wucewar ta inda zata.
________________________________________
AFTER 4 YEARS
Yara ne su biyar sanye da uniform na makarantar boko. Wando kalar ganye (green), sai rigar fara. Macen kuma doguwar riga ce daga sama fari sai k’asan ya kasance green.
Tafe suke a kan hanya daga makaranta zuwa gida, sabida korarsu kud’in makaranta naira d’ari uku da aka yi.
Sakina y’ar wajen Inna Murja wacce babu abunda ta rage daga hakinta sai ma ninka ta da tayi, sai tsalle-tsalle take yi. Duka-duka baza ta wuce 5 years ba.
Abubakar kuma na da takwas kasancewar gwarne aka yi tsakanin sa da Ahmadu. Don shi Ahmadu tara gare shi. Lawal kuma na da shidda. Umar kuma hud’u.
“Kai ku tsaya kuji! Tun da an koro mu kud’in makaranta, kuma jarabawa ake yi, kawai mu tafi wajen da Baba ke gyaran takalmin ko za mu samu ya bamu kud’in mu koma makaranta mu ma mu zana jarabawar.”
Gudu Sakina ta shek’a. Sai da tayi nisa sannan ta ce:
“Ni dai ba za ni ba. Bani son makarantar dama. Ku sai kun dawo.”
Tsautsayi ya saka Ahmad d’aukar dutse k’arami ya jefe ta dashi yana fad’in:
“Munafuka annamimiya!”
Sai dai dutsen na sauka a goshinta sai jini shaa. Duk da kasancewar dutsen k’arami ne amma tsini gare shi, shiyasa ya caki goshinta.
Wani irin ihuu ta tsala ganin yanda jinin ke zuba. Dafe goshin tayi tare da runtumawa a guje tayi gida.
Shi kuma Ahmad sai duk jikinsa yayi sanyi. Hannun k’annan sa ya kama suka nufi inda mal Bawa ke gyaran takalmin.
Kuna sauraron littafin: D’AN FAARI
Daga: Hausa Novel Dot Com
Kada ku manta ku yi:
Follow
Like
Share
Mun gode.
Zaune yake a kan wani d’an banci. Gabansa kuma wata lafiyayyar shinkafa da wake da miya, har da salat da kuma nawa guda uku a kai. Ga kuma ruwa mai sanyi na leda da kuma goran zob’o mai sanyi shima.
Ya kai loma ta uku kenan, kamar ance ya d’aga kai suka had’a idanu da y’ay’an nasa. Duk da sun gan shi, sun kuma ga abunda yake ci, sai yayi saurin tura robar abincin a k’asan bencin tare da d’aure fuska kamar an aiko masa da mala’ikan mutuwa.
Suna k’arisowa ya shiga fad’in:
“Uban mai kuma ya kawo ku nan? Laadi ce ta turo ku kuzo ku saka min idanuwa ko? To wallahi naji wani a cikin su yaje gida ya fad’i abunda ya ga ina ci, sai na ci ubanku nai maku dukun kawo wuk’a, kun ji ko baku ji ba?”
Gaba d’aya suka amsa da:
“Mun ji baba!”
Sai ya ce:
“Yauwa! To kuma uban mai ya kawo ku nan wajen?”
Ahmad ne yayi magana:
“Baba an koro mu kud’in makaranta ne, kuma jarabawa muke yi, shine muka zo karb’an kud’in.”
Har wani zazzaro idanuwa yayi tare da fad’in:
“Saboda uwar ku Laadi ta bani ajiyar kud’in! To ban da shi. Menene amfanin sana’ar da uwar taku take yi da baza ta iya cire kud’i ta biya maku ba? Shikenan babu taimako? Ai ba ni kad’ai ke da y’ay’an ba. Ku wuce ku bani waje dan uwar ku.”
Cikin sauri suka juya suka bar wajen. Umar kuwa kuka ya fashe dashi tare da juyowa yana fad’in:
“Baba zan ci abincin.”
Jifansa yayi da cokalin, sai da Ahmad yayi saurin janyesa suka zuba da gudu ganin yanda ya zaburo zai buge su. Sai da suka k’ule sannan ya fiddo abincin ya cigaba da ci yana karkad’a kai.
________________________________________
A can gida kuwa, da wani irin ihu da kuka Sakina ta shigo gidan.
Inna Murja da ke bayi tana wanka tayi saurin kwara sauran ruwan a jikinta, ko gama wankan bata yi ba ta d’auro zani ta fito tana fad’in:
“Wani wanda bai bid’ar albarkar iyayen ne ya tab’a min y’a? Ni fa y’ay’a na y’an so ne, kuma zan iya komai a kan su.”
Inna Laadi da ke zaune bakin k’ofa tana bakace ko kallonta bata yi, duk da tasan kuwa ita take wa habaici.
“Wayyoo Innar mu na shiga uku na lalace! Wayyo Inna ki cece ni jini na zai k’are!”
Da gudu Inna Murja ta k’arisa wajenta tare da saka hannu tana goge jinin da ya wanke mata fuska. Jikinta har rawa yake yi.
Inna Abu da Daada dake cikin d’aki suka yi saurin fitowa sabida ihun Sakinan da ya cika gidan. Hatta Inna Laadi sai da ta zo wajen ganin irin jinin da ke zuba a goshin Sakinar.
Ita ta wanke mata fuska tana yi mata sannu tare da saka mata toka a wajen. Sai bayan an wanke jinin ne suka ga ashe ciwon d’an k’arami ne, jinin ne kawai ya zuba da yawa.
“Wani d’an iskan ne ya miki wannan aikin haka Sakina?”
Fad’in Inna Murja, jikinta har rawa yake yi.
“Innar mu Ahmadu ne ya jefe ni da dutse don kawai nak’i bin su wajen Baba k’arbo kud’in makaranta.”
Wani irin ashar Inna Murja ta liliyo ta antayawa Ahmad d’in tare da fad’in:
“Wallahi yau gidan nan babu mai kwatarsa! Idan shi ya ga uwarsa bata k’aunar sa bata damu dashi ba, to ni na damu da y’ay’a na. Kuma wallahi baza ta sab’u ba. Bindiga a ruwa, yau sai na ga uban da ya tsayar masa gidan nan. Yau ko ni ko shi.”
Tun sanda Inna Murja ta kira sunan Ahmad, Inna Laadi ta bar wajen.
Inna Abu kuwa cewa tayi:
“Idan Amadun ya dawo, dan Allah kiyi kwad’on sa, kar ki bar shi da rai.”
Tana gama fad’in haka ta ja tsaki ta wuce.
Inna Murja kuwa kallon Daada tayi tare da fad’in:
“Daada kina dai ji ko? Yanzu kuma in kula ta, Jama’a su ce ban k’aunar zaman lafiya ko?”
Daada ta ce:
“Yi hak’uri ki kyale ta Murja. Kuma dan Allah ki bar maganar nan, kar ki hukunta Ahmadu, ni da kai na zan masa hukunci.”
Rik’e k’ugu Inna Murja tayi tare da fad’in:
“H’uhm! Cabd’ijam. Wallahi ki ma dai na maganar nan Daada, don wallahi sai na jibgesa kamar kayan wanki.”
“To ai shikenan tunda baza ki ji magana ta ba, kiyi yadda kike so Murja.”
Tana gama fad’in haka ta juya ta shige d’akin ta.
Dai-dai lokacin da su Ahmad suka yi sallama suka shigo gidan, da mugun sauri ta cafki hannun Ahmad tare da fad’in:
“Zo nan dan uwarka! Mai Sakina tayi maka ka fashe mata kai? Yau uban ka za ka ci cikin gidan nan!”
Kuna sauraron littafin: D’AN FAARI
Daga: Hausa Novel Dot Com
Kada ku manta ku yi:
Follow
Like
Share
Mun gode.
“Dan Allah Innar su Sakina kiyi hak’uri, wallahi tsautsayi ne, ba da gangan bane bazan s…..”
Ko kafin ya kai ƙarshen magana ta wanke fuskan shi da mari. Ta kuma wanke fuskan da mari hagu da dama. Tuni fuskan tayi fushi ta tasa, kuma sawayenta suka fito ral a fuskansa.
Bata hak’ura ba. Ta rik’a hannunsa har ɗakinta. Ta fiddo bulalan inji ta shiga zubaba masa ta ko’ina a jikinsa yana ihu.
Inna Abu kuwa ta tada sallah babu damar katsewa ta cece sa. Inna Laadi kuwa tana tsakar gidan amma ko kallo wajen bai ishe ta ba.
Sai da Inna Murja tayi masa rud’u-rud’u da jiki, sannan ta rik’a kanshi ta buga da bango sai da ya saki ƙ’ara sannan ya sume a nan ƙ’asa. Jini kuwa ya wanke fuskansa.
Dai-dai lokacin da Inna Abu ta idar da sallah, ko tsayawa addu’a bata yi ba ta kwasa a guje ta fito. Wani irin salati ta saki ta yo kan Ahmad da bai numfashi.
Hatta ita kanta Inna Murja ta tsorata ganin yanda Ahmad ya baje a ƙ’asa babu alamar rai.
Inna Abu fizgo Inna Murja tayi ta shiga dukanta tana kuka, har da cizo take haɗa mata. Mak’ota suka cika a gidan fam. Daga ciki ne aka samu wasu suka yayyafawa Ahmad ruwa ya farfaɗo tare da tsaida jinin da ke zuba a goshinsa wanda tuni wajen ya wani irin fushi ya kumbura.
Inna Laadi kuwa kamar bata gidan. Da yawan jama’a ma ita suke zagi suna mata masifa tare da fad’in:
“Kina zaune kina wawanci da shirme za’a kashe miki ɗa, kuma wallahi ke ce da asara!”
Da Inna Laadi taga surutun ya mata yawa sai ta mik’e ta fad’a ɗakinta ta turo kyaure.
Dambe kuwa tsakanin Inna Murja da Inna Abu, jama’a sun kasa rabawa. Wannan ta wawuro abu ta bugawa y’ar uwarta, ita ma y’ar uwar ta rarumo ta buga mata. Duk sun jima junan su ciwo.
Mal Bawa ne ya faɗo gidan yana muzurai tare da ratsawa tsakanin mutane har ya iso inda ake cakusa damben.
Inna Murja na ganin sa ta saki Inna Abu ta faɗi yaraf tana shure-shure tare da tara miyau a bakinta tana zubo dashi.
Hankali tashe Mal Bawa ya isa kanta ya shiga tofe-tofen yawu a fuskan don shi ba wani ilimin addini gare shi ba. Bismillah da kuma fatiha ita ma ba mai kyau ba kawai ya iya.
Ita kuwa Inna Murja sai bige-bigen ƙ’arya take yi tana fad’in:
“Mu za’a rik’a tauyewa hakk’i. Baza mu tab’a yarda ba sai mun ƙ’ona gidan na. Sai mun turo y’an uwan mu sun rusa gidan kowa ya mutu.”
Rud’ewa Mal Bawa yayi ya shiga rok’on Inna Murja.
Sauran mutanan da ke tsaye a kanta kuwa duk sun san cewa aljanun ƙ’arya Inna Murja take yi.
Inna Abu kuwa kanta ta dawo ta tsaya tare da fad’in:
“Kutumar kan babb…..kazan can ke da aljanun naki. Na ce idan kun fasa turowa an rushe gidan kowa ya mutu Allah ya shine muku har da sarkin aljanu albarka. Tsinanniya mara imani. Na fiki hauka. Ki gama aljanun ƙ’arya ki tashi, in kuma cin ubanki la’ada waje a nan wajen.”
A fusace Mal Bawa ya ce:
“Abu ashe baki da albarka ban sani ba. Ashe ke muguwa azzaluma ce ban sani ba. Gidan da muke cikin ne muna rufawa kan mu asiri ne kike fatan aljanu su rushe? To ta Allah ba taki ba.”
Sai ya juya ya kalli Inna Murja da har yanzu take harbe-harben ƙ’arya tare da fad’in:
“Allah huci zuciyar ku. Kar ku damu da Abu. Rashin hankali da hauka ne ke damun ta. Kuma yanzu zan yi maganin abun. Kar ku fusata dan Allah.”
Yana gama fad’in haka ya nuna Abu da yatsa tare da fad’in:
“To kije gidan ku na sake ki saki uku. Har abada ba ni ba ke. Da ma duk cikin mata na kece annoba bala’er iya jarababbiya. Kin bin kin takura min, kin takurawa matata. To yau dai na yar da kwallon mangwaro na huta da ƙ’uda.”
Gaba ɗaya jama’ar wajen suka ɗauki salati suna tafi da hannu.
“Duk ku fita y’an bura uba ku bar min gida kafin na watsa ku!”
Fad’in Mal Bawa.
Gaba ɗaya suf-suf suka bar gidan suna zaginsa a zuciya.
Inna Abu kuwa ɗaki ta shiga ta tattare kayanta tsaf. Wanda zata iya ɗauka ta fito dashi tare da kulle ɗakin ta.
Sannan ta jawo Ghana-must-go ɗin da ta fito dashi ta hau jaa.
Da gudu Ahmad ya nufe ta ya ruk’unk’ume ta ya fashe da kuka yana fad’in:
“Dan Allah Inna kar ki bar ni a gidan nan. Ki tafi dani duk inda zaki. Ke kadai ce kike sona.”
Kuna sauraron littafin: D’AN FAARI
Daga: Hausa Novel Dot Com
Kada ku manta ku yi:
Follow
Like
Share
Mun gode.
Bata so tayi hawaye, amma sai da suka zubo saboda tausayin Ahmad da ya kamata.
Ajiye Ghana must go d’in tayi tare da nufar ɗakin Inna Laadi ta hankad’a labule. Kasa kallonta Inna Laadi tayi. Har ciki ta ƙaraso ta tsaya a kan Inna Laadin tare da fad’in:
“To ni Allah yayi zama na da ku ya ƙ’are a cikin gidan na. Sauran kuma ya rage gare ki. Ko ki cire banzar al’ada da ɗabi’ar da kika ɗaurawa kanki ki rungumi ɗan ki, ko kuma kiyi dana sani da asara mafi muni a kaf rayuwar ki.
Shawara na baki, domin yanzu tarbiya da rayuwar ɗan ki zai koma wani hannun. Idan kin jawo sa jiki ya tsira, idan kuma kin banzatar dashi kamar yanda kika saba ruwan ki.
Ni kin ga tafiyata ta har abada. Ban sani ba ko zamu sake haɗuwa. Kin fi kowa sanin bani da kowa a garin Zariya. Daga Caranci aka auro ni, kuma yanzu haka can nayi. Allah ya bamu alheri.”
Tana gama fad’in haka ta fito daga ɗakin tayi wajen kayanta ta ɗauka ta nufi kwar gida.
Da mugun gudu Ahmad ya bita yana wani kuka yana jan Ghana must go d’in yana kuma rok’onta akan ta tafi dashi.
Bulalan da Inna Murja ta dake shi da ita, ita Mal Bawa ya ɗauka ya shiga tsula masa a kan ƙ’afafunsa yana korasa gida. Amma Ahmad haka ya dunga ihu yana bin bayan Inna Abu.
Mak’ota suka firfito daga gidajensu suna kallon abunda ke faruwa, wasu har da kwallar su.
Mal Bawa da yaga cewar idan bai yi da gaske ba duk inda Abu ta saka ƙ’afa nan Ahmadu zai saka, sai ya dadumeshi yayi ta jan sa har cikin gida. Sannan ya haɗa ƙ’afafunsa da hannayensa ta baya ya ƙ’ulle ya bar shi nan tsakar gida yayi ficewarsa.
Rana ta kwallo sosai. Duk da kuwa anyi sallar azahar, amma irin ranar nan ne mai gasa jikin ɗan Adam.
Gashi ƙ’afarsa da hannaye a ƙ’ulle ta baya. Babu damar da zai iya kwance ƙ’afar dan ba ƙ’aramin ƙ’ullin Mal Bawa yayi wa ƙ’afar ba.
Daada na ɗaki balle ta fito ta cece sa. Inna Murja kuwa na kwar ɗakin ta tana kallonsa yana ihu da kuka.
Ahmad da azaba ta ishe sa ya shiga kwalla kiran mahaifiyar sa yana fad’in:
“Innar mu! Innar mu zan mutu! Dan girman Allah ki taho ki kwance ni. Na shiga uku Innar mu.
Dan Allah ki kwance ni in dawo inuwa. Wallahi na miki alk’awari idan wani abu nake miki daga yau ba zan sake ba. Duk abunda kika ce in yi shi zan yi.
Dan girman ubangiji ki min afuwa kizo ki kwance ni. Wayyo Allah! Inna Abu ki dawo wallahi kashe ni za ayi a cikin gidan nan.
Inna Murja dan Allah ki zo ki taimaka min ki kwance ni. Wallahi daga yau bazan ƙ’ara tab’a Sakina ba. Dan Allah ki kunce ni.
Ni na yarda bayan kin kunce ni kiyi ta duka na har sai kin gaji. Amma dan Allah ki kunce ni in bar cikin rana. Wallahi dahuwa nake yi!”
Wani irin dariya Inna Murja ta kwashe dashi tare da fad’in:
“Uwar ka ma da ta tsuguna ta haife ka bata zo ta kunce ka ba, sai ni ce zan kunce ka? Baka da hankali! Ka mutu a wajen.”
Ahmad ihu ya cigaba da yi yana fad’in:
“Innar mu dan Allah, dan iyayen ki ki zo. Ko baza ki kunce ni ba, ki zo ki mai da ni cikin inuwa dan Allah!”
Innar tana cikin ɗaki kuma tana jinsa, amma ko gezau. Kuma ko a fuskanta babu tausayin Ahmad ɗin.
Abubakar ne ya fito daga ɗakin ya nufo kansa don ya ƙ’ok’arta kwancesa, amma sai Inna Murja ta daka masa wani tsawa tare da nuna sa da bulala tana fad’in:
“Kul! Wallahi hannunka ya tab’a sa, idan baban ku ya dawo sai na fad’a masa kai ma anyi maka irin yanda akai masa.”
Komawa gefe Abubakar yayi yana kallon Ahmad ɗin yana kuka…
Sai mun haɗu a next page. But comment, Like da kuma Share ɗin ku shi ke Sani Jin Karsashin yin saurin suburbuɗo muku wani page ɗin!