Skip to content

Hausa Novel

My WordPress Blog

D’AN FAARI Complete

Posted on April 3, 2026April 3, 2026 By Maiallura No Comments on D’AN FAARI Complete

D’AN FAARI
PAGE 2
Daga: Hausa Novel Dot Com


Ko da Safara’u ta fito daga d’akin Inna Laadi, suf-suf ta fice daga gidan har da ɗan haɗ’awa da gudu. Kicib’is suka ci karo da Inna Abu, ita kuma dawowar ta kenan daga kasuwar Laraba, sai da ta bangajeta kasancewar bata ga zuwan ta ba.
“Ke, wannan wani irin iskanci da rashin hankali ne haka? Ba kya gani ne? Wannan ai iskanci ne! Wallahi da kin min b’arna, kin wa billahil sai kin biya ni kaya na, na fiki hauka wallahi!” Dad’in Inna Abu tana hararar ta kamar idanunta zai faɗo ƙasa.
“Yi hak’uri Abu, wallahi wani bala’in da gujewa daga cikin gidan ku. ɗan kishiyar ki ne ya karye, ko kuma in ce miki uwarsa ta karya sa, kuma ko kallon inda yake bata yi ba, kuma ko da na shigo na iske Murja a tsakar gida tana yankar farce, amma ko kallon inda Ahmad ya ke bata yi ba. Shine fa na ɗauki ɗan na yi d’akin Laadi domin in ganewa idanuwana shin tana gidan ko bata nan, sai kawai na iske ta kan gado tana ninkin kaya. Da na fara yi mata k’orafi, sai kawai gani na yi ta fice daga d’akin ta barni rik’e da yaro yana ihu a hannuna. To shine ni ma na ajiye sa a nan d’akin, na yi fitowa ta gudun yaro ya zo ya mutu a hannuna, a ce ni na kashe sa, hukuma ta kama ni. Shiyasa kika ga na yi irin wannan fitowar har ina k’ok’arin yi maki b’arna.”
“Inna lillahi wa’inna ilaihir raju’un! Shi Ahmad ɗin ne ya karye a hannu? Na shiga uku!” Fad’in Inna Abu tare da shiga cikin gidan da sauri. A tsakar gida ta ajiye kayan tare da fad’awa d’akin Inna Abu inda take jiyo kukan Ahmad ɗin har muryarsa ta dishe.
D’ago sa ta yi, tare da sakin salati ganin hannunsa na lilo. Cikin sauri ta fito daga d’akin ta yi hanyar waje, ko bi ta kan kayan da ta shigo dasu bata yi ba. Inna Laadi kuwa tana ganin fitarsu, sai ta yi saurin shigewa d’akin ta, ta ci gaba da ninkin kayan yara da take yi. K’arya ne ka kalli fuskarta ka ce ka ga wani alamu na tashin hankali ko tausayi a idanunta, ko a jikinta ta ci gaba da abunda take yi.
Inna Murja kuwa, tana ganin fitar Inna Abu, ta yi saurin fitowa daga d’akinta gaba ɗaya, tayo wajen kayan Inna Abu tare da soma bubbud’e ledojin. Ledan magi star ta ɗauka guda ɗaya, farin magi ma leda ɗaya ta ɗauka, tare da lokan garin kuka, barkono da fulawa loka uku da Inna Abu ta sayo don yin taliya y’ar murji. Ta yi d’aki da sauri har da turo kyaure tana murmushi.
Inna Abu kuwa, tun da ta ɗauki Ahmad bata tsaya ko ina ba, sai gidan Murtala Wanzan dake can ƙasan layinsu. Ko da taje bata sa me shi ba, sai da aka tura ɗan sa yaje yayi kiran sa sannan suka dawo tare da ɗan nasa.
Kallo ɗaya ya yi wa hannun Ahmad ya ce:
“Subuhanallah! Yaya aka yi wannan yaron ya samu karaya haka har guda biyu a hannu?”
Inna Abu na sharar hawaye ta soma magana:
“Dawowa ta kenan, na jiyo ihunsa daga cikin gidan, ban san mai ya same shi ba. Dan Allah a duba masa hannun sai a ɗaura sa.”
Karb’an Ahmad yayi daga hannunsa tare da fad’in:
“Kud’in ki dubu takwas, a haka ma wallahi Abu, dan ma kece da kuma tausayin ƙaramin yaron nan.”
Inna Abu ta ce:
“Babu komai, duba masa hannun dan Allah! Allah sarki Ahmad, kai dai Allah ya had’aka da sakaryar uwa wallahi.”
Fad’in Inna Abu tana sharen kwalla. Kai hannu kawai wanzamin nan yayi kan hannun Ahmad ya saki wani ƙaran da sai da Inna Abu ta yi maza ta bar wajen ta shige d’akin ɗaya daga cikin matan Wanzan. Ahmad kuwa har da kashi sai da ya yi tsabar azaba.
Bayan an gama d’orin, wanzan ya fad’a mata abubuwan da za’a kiyaye don ya yi saurin warkewa.
K’irgo dubu hud’u da dari biyu ta yi tare da mik’a masa, tana fad’in:
“Dan Allah ka yi hak’uri da wannan, shi kaɗai ne ya rage min a jikina. Dawowa ta kenan daga kasuwa na taras da wannan abu, in sha Allah nan da kwana biyu ko uku zan kawo maka cikon kud’in ka.”
Ba tare da damuwa ba ya ce mata babu komai, ita kuma ta sab’a Ahmad da ke ta ajiyar zuciya a kafad’a suka yo gida.
Kuna sauraron littafin: D’AN FAARI
Daga: Hausa Novel Dot Com
Kada ku manta ku yi:
Follow
Like
Share
Mun gode.

Da butan da ke tsakar gida ya fara ball sai da ta daki jikin bangon ginin ƙasa sannan ta watse a ƙasa a fashe saboda dama ta kanta butar ta mugun jin jiki, kuma da ita y’aran gidan suke uzuri.
“Wata shegiyar mata ce a cikin ku ta lalube min wando ta ɗauki naira dubu da hansin ɗin da ita kenan ta rage min cikin jikina? Na ce wata shegiyar ce?” Fad’in Malam Bawa yana kallon ko wani ɗakunan matansa.
Inna Murja ce ta soma fitowa tana sakin hamma, domin ba ƙaramin yunwa take ji ba, kuma ba ta da ko sisi, kuma tsoran girki abin da ta sata take yi, don ta san dole Inna Abu ta gane ita ta ɗauka idan har ta yi girki. Gashi kud’in Mal Bawan da ta kwashe da safe, zibin da shi tayi. Fuska a washe ta soma magana:
“Ah Malam, ka dawo! Sannu da zuwa, daman kuwa kaman ka san kai nake jira.”
Malam Bawa kamar zai watsa mata harara, sai kuma ya fasa don ya san ƙaf gidan wajen ta be kawai zai iya samun kud’i. Sai ya ce:
“Murja, ki koma ɗaka, don ba dake nake yi ba, da Zainabu da Laadi nake yi, ko su fito min da kud’i na, ko kuma wallahi kin ji na rantse, kun yi wa kud’in cefanen su na sati guda.”
Malam Bawa na ida zancen sa, Inna Abu na kunno kai cikin gidan, kuma komai a kunnanta ya sauka.
Wani kallo Malam Bawa ya bi Inna Abu da shi dama duk cikin gidan, ita ce abokiyar fad’an sa, Inna Laadi ko bi ta kansa ba ta yi, balle ta kula sa. Ko yanzu haka tana ɗaka tana jiyo shi, amma ko motsi bata yi ba daga inda take, balle kuma ta fito har tayi sa’in sa dashi.
“Yauwa! Ke kuma daga gidan uban wa kike da ɗa sab’e a kafad’a? Ko da yake ni minene damuwa ta, abunda na sani shine kawai a cikin ke da Laadi tabbas wata ta caje jiki na ta ɗauke min dubu da naira hamsin, kuma ko a biya ni, ko kuma kun yi wa kud’in cefanen ku na sati guda, ehe!”
Jikin Inna Abu har tsuma yake yi. Tabarman dake shimfid’e a kusa da ƙofar ɗakin Inna Laadi ta shimfid’e Ahmad sannan ta dawo ta tsaya gaban Malam Bawa, tare da tsira masa hannu a goshi sannan ta soma magana:
“Ka ci uwar rainin hankali da wayo Mal! Kalle ni da kyau, na yi maka kama da wacce zata ɗauki kud’in ka? Ka dai koma kayi tunanin inda ka shiga har aka caje aljihun naka aka kwashe kud’in ka. Har kana wani buɗe baki kana fad’in mun yi wa kud’in cefanen mu na sati, sai ka ce dama kud’in cefanen kirki kake bamu. Bayan idan Allah yayi mu ka ɗan samu ɗari biyu a hannun ka wanda a sati biyu bai wuce sau ɗaya ba, to ba ƙaramin sa’a muka yi ba. Allah ma ya ƙara da aka sace kud’in, alhakin mu ne mu da yara, kuma wallahi kar ka ƙara sa mana sata, da ka fita yau daga wani ɗaki ka fita? Ni dai na san ba ni ce da girki ba, kuma Laadi ma haka.”
“Ke! Wallahi kar ki fara! Don naga kina ƙoƙarin ƙala min satan, ko da yake an ce dama tabarmar kunya da bori ake nad’e ta. Kuje can ku fiddo masa da kud’in sa tun kan dare ya muku.”
D’aga hannu Malam Bawa yayi tare da fad’in:
“Haba Murja, haba! Ke har sai kin tsaya kina sa’in sa da ita, ai ina kallon kwayar idanunta na tabbatar ita ta saci kud’in nan. Don na shiga ɗakin ta har take tambayata zata fita zuwa kasuwar Laraba, don haka tabbas ita ta ɗauki kud’in nan, kuma sai kin biya ni.”
“Bawa, na ɗauka! Na ce na ɗauka, kuyi duk abunda za ku yi kai da b’arauniya matar taka wacce b’atar basira ya saka ka kasa gane ita ɗin wacece tun tuni. Mun riga da mun san halinta, tantiriyar munafuka kuma b’arauniya ce.”
A fusace, Inna Murja ta ce:
“Ubanki na sata? Na ce wannan shagid’ad’d’an tsohon mai kama da wanda cutar sida (AIDS) ta cinye sa!” Ta fad’i tana hararar Inna Abu tare da rik’e ƙugu.
“Uban nawa ne mai kama da wanda cutar sida ta cinye sa? Wallahi sai na kakkarya ki cikin gidan nan!” Fad’in Inna Abu tare da yin kan Inna Murja suka kaure da dambe. Kuma Inna Abu, irin matan nan ne masu ƙaramin jiki amma akwai ƙarfi kamar doki, duk da ta yi biyunta, sai da ta kai ta ƙasa ta hau kilarta.
Kuna sauraron littafin: D’AN FAARI
Daga: Hausa Novel Dot Com
Kada ku manta ku yi:
Follow
Like
Share
Mun gode.

Da Malam Bawa yake tsaye, wani tsohon bokitin ƙarfe dake gindin rijiya ya ɗauko, dare da zama a kai ya soma bugun ƙasan bokitin yana faɗin:
“Ku casu, ku casu ba mai raba ku! Hooo ni Sulaimanu Bawa, sai ni na Laadi da Abu angon Murja! Yanzu duk cikin fad’in unguwar nan, wanene ake faɗa a kansa idan ba ni ba!”
Haka ya ɗun ga kuranta kansa. Su Inna Murja kuwa sai faman dambe suke yi. Da taga fa tabbas Inna Abu za ta iya yi mata illa, sai ta shiga ihu tana kiran jama’a. Duk abin nan da suke yi, Inna Laadi tana ɗaka tana ji, amma ko lek’e.
Mak’ota ne suka fara shigowa, sai dai duk wanda yayi arba da Mal Bawa yana kid’i da bokitin ƙarfe, sai ya saki baki yana salati. Dakyar aka janye Inna Abu a kan Inna Murja, wacce sai kuka take yi wiwi tana faɗin:
“Ku bar ta ta kashe ni a kai wa iyayena gawa! Dama na jima da sanin kina mugun bak’in cikin gani na a raye, don haka ku bar ta ta kashe ni kawai.”
Mal Bawa kuwa dariya yake har yana riƙe ciki yana faɗin:
“Ki bar su, abinci suka ci suka ƙoshi, ni ai ina son irin wannan wasan, ina kallo ina jin nishad’i.”
Nan jama’a da dama suka shiga tur da halinsa, wasu kuma suna faɗin: “Allah ya shirya!”
“Lahaula wala’quwata! Dama na faɗi wannan yaro karyewa yayi a hannu, Allah sarki har an gyaro hannu. Sannu kaji Ahmadu!” Fad’in Safara’u har da ƙoƙarin matso hawaye. Sai a lokacin Mal Bawa ya lura da hannun Ahmad, sai kuma ya mai da kallonsa izuwa wajen Inna Abu dake cika tana kumbura, don taso sai ɗaki Inna Murja sosai ko za a cece ta.
“Abu, ke na gani ɗauke da Ahmadu, mi ya same sa? Garin yaya ya karye a hannu?” Ya faɗi hakane yana mai k’arisawa kusa da Ahmadu wanda har ya farka daga baccin azabar da ya soma ɗaukarsa sakamakon uban damben da Inna suka ci da junansu.
Harara ta maka masa tare da faɗin:
“Sai ka tambayi mahaukaciyar mahaifiyar ta sa kaji yadda aka yi yaji ciwo.”
Mik’ewa yayi a zafafe tare da nuna ta da hannu yana faɗin:
“Ke iskanci ki ya tsaya! Iya mata na kar ki sake kice za ki min shi, don sai in kaɗa ki gidanku. Ya zan tambaye ki? Ki tsaya kina harara na tare da faɗa min baƙ’ar magana. Iskancin banza da wofi!”
“Idan har aka zo wajen ka an zo basto (bus stop), don duk garin Zariya ban ga irin ka ba. Abinci bai ishe mu, tsikari duk ya bi ya ishe mu, wannan wani irin bala’i ne haka, a’ah!” Faɗin Inna Abu.
“Bala’i! Ni ne bala’in Zainabu? Zainabu! Zainabu!! Zainabu!!! Sau nawa na kira sunan ki? To wallahi ki kiyaye ni, tom!” Ya faɗi hakane tare da hankad’a labulan Inna Laadi, wacce ke zaune a ƙasa tana k’ulla manja a farar santana.
“Munahika almura! Sai ki riƙa yin abu kamar mutuniyar kirki nan kuwa ta banza da wofi ce! Yo to ta banza da wofi mana. Yau kuma uban mi ki kai masa har ya yi sanadiyar karyewarsa a hannu?” Ya faɗi yana kallonta, duk da kuwa ya san ko da zai shekara a tsaye a wajen ba za ta yi ko da tari mai ƙarfi ba, in dai akan Ahmad yake mata magana, ba shi ba, ko wanene idan zai yi mata maganar Ahmad baza ta taɓ’a bashi amsa ba.
Domin akwai wani lokaci, duka shekarun Ahmad ɗaya da wata bakwai, yana wasa gindin rijiya, kuma saura kaɗan ya faɗa sai Allah ya turo da wata mata ta zo ɗiban ruwa a gidan, ta yi saurin k’arisawa ta riƙo sa. Ya kuwa tsandara ihu sabida ya tsorata, matan ta shiga kwad’a sallama a gidan tana tambayan ɗan waye. Inna Laadi kuwa tana kallon komai a window. Tun kafin matar ta shigo, amma kunyar D’AN FAARI ya saka ta tak’i fitowa, gudun kada wani ya shigo ya ga ta je ceton D’AN FAARI, zai faɗa rijiya.
Matar ta hankad’a labule su kai ido biyu da Inna Laadi, sai ta saki salati don a tunanin ta Ahmad ba ɗan ta bane, ɗan kishiya ne. Shiyasa tak’i fitowa. Nan kuwa ta shiga surfa bala’i da masifa, har wasu suka shigo gidan, way’en da suka san Inna Laadi ita ce mahaifiyar yaron, kuma suka shaida mata.
Baki sake matar take kallon Inna Laadi. Daga ƙarshe, tsabar takaici, matar ta fashe da kuka tare da dangwarar da yaron a nan ƙasa ta fice daga d’akin, don ji take zata iya rufe Inna Laadi da duka idan ta ci gaba da tsayuwa a cikin d’akin. Ruwan da bata ɗiba ba, kenan, ta fice daga gidan.
Kuna sauraron littafin: D’AN FAARI
Daga: Hausa Novel Dot Com
Kada ku manta ku yi:
Follow
Like
Share
Mun gode.

Kwafa Malam Bawa yayi tare da sakin labulan, ya juya tare da ficewa daga gidan, ko kallon Ahmad bai sake yi ba, gudun kada a tambaye shi kud’in gyaran hannun yaron.
Inna Abu ce ta fito daga ɗaki da sauri, tana zuba salati tare da faɗin:
“Wallahi ba haka na ajiye kaya na ba! An min sata cikin gidan nan—loka uku na fulawa da zan yi taliya y’ar murji, ledan magi star da fari babu, har da kukan da na sayo zan k’ulla. Wallahi, da sake a gidan nan, dole a fito min da kaya na, tun da babu shegiyar da ta bani jari lokacin da na fara sana’a ta.”
Tana gama faɗin haka, ta faɗa ɗakin Inna Murja tare da miƙa mata hannu:
“Fiddo duka kaya na da kika ɗauka ki bani tun muna shaida juna, ko kuma in canza maki kamanni yanzu. Ni ba Laadi bace da za ki yi wa abu ta kyale ki—Zainabu Abu nake!”
Duk da Inna Murja a tsorace take da Inna Abu, sai ta daure ta soma magana da tsawa da ihu:
“Ba na gane in fiddo maki kayan da na ɗauka ba! Yaushe na ɗauki kayan naki? Kin ganni ne ko kuma wani ne ya gan ni ha faɗa miki? Allah ya isa tsakani na da ku, da kullum kuke bi na da sharrin sata. Wallahi ba zan yafe maku ba, kuma sai Allah ya mana shari’a ranar gobe.”
Inna Abu ta yi harara tare da faɗin:
“Ko kin faɗa, ko baki faɗa ba, tabbas sai Allah ya mana hisabi, ba ma ni kaɗai ba, har da sauran mutane da kike wa sata, ehe! Fito min da kaya na kawai tun muna shaida juna.”
Tsabar ƙarfin hali irin na Inna Murja, taƙi fito da kayan. Inna Abu ta caje ko ina amma bata ga kayan ba; babu inda bata hargitsa ba a ɗakin. Hakane ya saka ta kalli Inna Murja tare da faɗin:
“In Allah ya yarda, sai an kama ki dai dai kin kai hannu a kan kayan mutane zaki ɗauka, kuma a cikin dubban mutane ta yanda kowa zai gane asalin koke wacece. Bazan taɓa yafe miki kaya na da kika ɗauka ba!”
Tana gama faɗin haka ta fice daga ɗakin.
Inna Murja kuwa ta ɗaga murya tare da faɗin:
“Ni ma sai Allah ya mana hisabi na ƙazafin da kika min!” Amma kuma ƙasa-ƙasa sai cewa tayi:
“Ke kin isa in yi ajiya ki gani, to cikin kayan wanki na k’ulle! Kuma wallahi sayar dashi zan je in yi yanzu, in samu kud’in da zan saya abinci muci ni da y’aya na.”
Inna Abu, da zuciya tayi a kan ba za ta kuma kula Ahmad ba, ko hakan zai saka Inna Laadi ta yi hankali, amma da ta tuna ko wacece Laadi, sai kuma ta fito hannunta rike da robar abinci mai ɗauke da fara, mai da yaji-yaji, da man k’uli.
Yana nan kwance a kan tabarma, amma kallo ɗaya zaka masa ka san ba ƙaramin jin jiki yake yi ba. Bini-bini yake durza bayansa a kan tabarma saboda rad’ad’in da bayan yake masa. Baccin ma a mugun wahale yake yin sa.
K’arisawa Inna Abu tayi tana jin matsanaicin tausayin yaron a zuciyarta. Ajiye kwanon tayi a gefe, tare da ɗan buguwa ƙafarsa, sai ya buɗe idanunsa.
Mik’ar dashi zaune tayi, tare da jingina shi da bango, amma sai ya fashe da kuka, shigewa jikinta, yana kuma so ya kai hannunsa mara ciwo zuwa bayansa.
A hankali, Inna Abu ta kware rigar, gabanta ne yayi wani irin mugun bugawa lokacin da tayi arba da bayan jazurr Ahmad kasancewar sa fari. Sannan ka kwarkwasa sama da ashirin sun manne a bayansa suna manna masa cizo…
________________________________________
Sai mun haɗu a next page.
Ka tuna: Comment, Like, da kuma Share ɗin ku shi ke Sani! Jin karsashin yin saurin suburbuɗo muku wani page ɗin!

Pages: 1 2 3 4
Uncategorized

Post navigation

Previous Post: GIDAN UNCLE Complete

Related Posts

GIDAN UNCLE Complete Uncategorized

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Archives

  • April 2026

Categories

  • Uncategorized

Recent Posts

  • D’AN FAARI Complete
  • GIDAN UNCLE Complete

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on GIDAN UNCLE Complete

Copyright © 2026 Hausa Novel.

Powered by PressBook Masonry Blogs

Powered by
►
Necessary cookies enable essential site features like secure log-ins and consent preference adjustments. They do not store personal data.
None
►
Functional cookies support features like content sharing on social media, collecting feedback, and enabling third-party tools.
None
►
Analytical cookies track visitor interactions, providing insights on metrics like visitor count, bounce rate, and traffic sources.
None
►
Advertisement cookies deliver personalized ads based on your previous visits and analyze the effectiveness of ad campaigns.
None
►
Unclassified cookies are cookies that we are in the process of classifying, together with the providers of individual cookies.
None
Powered by