Skip to content

Hausa Novel

My WordPress Blog

D’AN FAARI Complete

Posted on April 3, 2026April 3, 2026 By Maiallura No Comments on D’AN FAARI Complete

D’AN FAARI
PAGE 1
Daga: Hausa Novel Dot Com


Wata kyakkyawar budurwa ce wacce a kalla za ta kai shekaru ashirin da ɗaya zuwa ashirin da biyu, sanye cikin wando palazzo kalar fari fat, sai wata riga armless ita ma fara tass ta kuma kwanta a kan fatar jikinta, irin kyawawan yaran nan ne wanda za ku gan su kamar su suka halicci kan su don tsabar kyawu. Sosai take da ƙirar jiki irin figure 8 ɗin nan, kyakkyawa gaske ce mai ɗan duhun fata wato irin chocolate colour ɗin nan, sai dai skin ɗin ta wani irin shining da glowing yake yi, kana kallon fatanta ka san ba ƙaramin gyara da kula yake samu ba. Tana da gashi sosai a kanta, kuma ba ƙaramin ji da gashin take yi ba saboda duk bayan 2weeks tana shagon saloon domin gyara.
Wani irin dogon takalmi kalar silver ne a ƙafarta, sai kuma wani farin siririn gyale da ta yi a cuci da shi yayin da uban tulin gashinta ya fito ta ƙarshe. Wani ɗan ubansu fashion bag ne a hannunta ɗan ƙarami kalar silver, baƙin tinted glases ɗin dake kan fuskanta kuma ta ɗan sauko da shi kaɗan kan dogon hancinta tana taunar cingam ƙas-ƙas-ƙas. Babu abin da kake ji sai ƙarar takalmin ta yayin saukowarta daga stairs.
Daddy, momma, Shuraim, Suhail da Sauban dake kan dinning suna yin dinner, gaba ɗaya suka zuba wa stairs ɗin idanu. Sai da ta gama saukowa gaba ɗaya ta nufo wajen sannan momma ta ɗauke kanta tana mai jujjuya spoon, ta kuma kasa ƙara kai loman abinci a bakinta.
Su Shuraim da Daddy kuwa gaba ɗaya suka haɗa baki wajen faɗin,
“Wow!”
Shuraim mai bi mata ya ce,
“Wow! Akeela kin gan ki kuwa, looking beautiful. Ina za ki je ne?”
Sai da Akeela ta yamutsa fuska sannan ta ce,
“Party muka haɗa na kammala degree ɗin mu. We guys are going to have fun!”
Ta faɗa tana wani irin faarr da idanu.
Gaba ɗaya kallon momma suka yi wacce ta ajiye cokalin hannunta da ƙarfi tare da folding hannunta tana kallon Akeela tun daga sama har ƙasa, irin kallon you’re out of your sense.
Zarowa momma idanuwa Akeela ta yi tare da faɗin,
“What again momma? Are you going to stop me? I’m glad daddy is here to stop you from what you’re trying to do!”
Ta faɗa a tsiwace, cike kuma da rashin kunya tare da rashin tarbiya.
Ita ma momma a fusace ta ce,
“Akeela! You’re not going anywhere, and that’s final. Idan kuma ke kika haife ni, za mu gani yau. Kina hauka ne? Kalle ki fa kamar ba ’diyar musulmai ba. Na riga na gama magana, you are not going anywhere!”
A zafafe ya miƙe har yana buga glass ɗin dinning ɗin da ƙarfi tare da faɗin,
“Ke Fauza ki kiyaye ni a kan ’ya’yana! Wai me yasa idan har na miki warning a kan ’ya’ya na bai shiga kunnuwan ki ba? Wallahi, tallahi zan iya miki abin da baki taɓa tunani ba a kan ’ya’ya na Fauzah! Akeela will go to the party, and that’s final, sai in ga ni da ke waye ya isa, kuma wanene shugaba a cikin gidan nan!”
Akeela kuwa kukan ƙarya ta soma yi tana bubbuga ƙafa a ƙasa tare da faɗin,
“Daddy ban san me yasa momma ta tsane ni ba, bata sona kamar ba ita ta haife ni ba, and kuma fa I’m THE FIRST BORN, abubuwan da take min zai iya sa su Shuraim su raina ni fa. Kuma wai ba zan je party da na kashe kuɗi wajen haɗawa ba, ni wallahi sai na je ko ta bar ni ko bata bar ni ba.”
Ta ƙarisa maganar tana murguda baki har da ɗan harara ƙasa-ƙasa.
Jawo ta jikinsa ya yi tare da faɗin,
“Come on don’t cry Akeela! Ta isa ma ta hana ki, ke za ki yi driving ko kuma a kai ki kike so a yi?”
Ɗan turo baki Akeela ta yi tare da faɗin,
“Ni zan yi driving da kai na.”
Shafa kanta daddy ya yi tare da faɗin,
“Ki na buƙatar wani abu ne?”
Girgiza kai Akeela ta yi tare da faɗin,
“I have money dad. Ni dai ka ce momma ta bar ni in tafi, my friends are their waiting for me, I have to go.”
Hanya Daddy ya nuna mata tare da faɗin,
“You can take your leave my dear, no one can stop you, I mean no one!”
Gaba ɗaya sauran yara suka shiga ihu suna faɗin,
“Daddy’s girl! Oh you can go to the party sis, dad means it. You no, when he said yes, he mean yes and nobody on the earth can change it, just take you leave babe.”
Momma kuwa zuciyarta har wani tafasa yake yi tsabar baƙin rai, bata san lokacin da ta isa gaban Akeela ba tare da faɗin,
Kuna sauraron littafin: D’AN FAARI
Daga: Hausa Novel Dot Com
Kada ku manta ku yi:
Follow
Like
Share
Mun gode.

“Wallahi Akeela if you take step za ki ga abin da zan miki cikin gidan nan!”
Sai kuma ta juya ta kalli daddy tare da faɗin,
“Wai me yasa kake min haka ne daddyn Akeela? Ya kullum ina tufka kai kuma kana warwarewa? Ka san yadda ake zagin mu a gari kuwa akan tarbiyyar ’ya’yan mu? Must especially Akeela! Kar ka manta ita mace ce, kuma gidan wani za ta je, idan har bata da tarbiya, ta ina za ta iya bai wa ’ya’yan da za ta haifa nan gaba tarbiya?
Na gaji, I’m tired Ahmad Sulaiman Bawa! I’m tired of yadda nake ƙoƙarin bai wa ’ya’ya na tarbiya kai kuma kana rushewa ba. Kalla fa, kamar Akeela, a cikin wannan shiga, at this hours ta buɗe baki ta kalle mu, mu iyayen ta, ta ce mana wai za ta party saboda kawai ta kammala degree!
Mutane nawa ne kamar ta a titi suna neman masu tallafa musu domin samun ilimin da ta samu, amma ita ta samu kuma shi ne za ta gode wa ubangiji ta wannan hanya? Har kuma kake bata go-ahead ta je party suna raye-raye da shaye-shaye da maza da mata ko?
To ni ba zan amince ba, Akeela will not go anywhere!”
Ta ƙarisa maganar da ƙarfi tana kallon ’ya’yan nata dai-dai.
Sai da daddy ya matso har gabanta suna jin ƙamshin juna, sannan ya saka idanuwansa a cikin nata tare da faɗin,
“Who are you da har zan yanke hukunci a kan ’ya’ya ki ce ke bai miki ba?”
Zuciyar Momma a ɗake ta kalli cikin idanunsa tare da faɗin,
“Mother! Ina nufin mahaifiyarsu, wacce take ganin hanyar da ka bullo ba mai bullewa ba ce!”
Ɗan yatsa ya ɗaga ya nuna Akeela da shi tare da faɗin,
“Wannan ’yar yarinyar ce kike wa fatan shaye-shaye kuma har kike kiran kan ki da her mother? Mother ce za ta yi wa ’yarta wannan fatan? Wai anya Fauzah kina ƙaunar Akeela kuwa? Wallahi I will never let what happened to me, to happen to my own daughter, never! Tarihi ba zai taɓa maimaita kansa a kan ’yata ba. Kuma na gama magana, Akeela will go to the party!”
Yana gama faɗin haka ya finciki hannun Akeela tare da nufar ƙofa.
Da gudu Momma ta sha gabansu tana kuka tare da faɗin,
“Akeela ba za ta fita ba, babu inda za ta je!”
Ƙugu daddy ya kama, sai kuma ya kalli gefe da gefe, tare da ɗaga hannu ya wanke fuskar Momma da shi, sai da ta zube a ƙasa tare da dafe kuncinta.
Da sauri Akeela ta ɗaura hannu a bakinta tana waro idanuwa.
Su Shuraim kuma bayan mamaki sai kuma suka fashe da dariya suna nuna Momma da hannu.
Akeela kuwa sai ta ji duk jikinta ya yi sanyi, sai ta yi wani irin tana kallon mahaifin nata.
Momma kuwa wani irin kuka ta fashe da shi tare da faɗin,
“Ni ka mare? Ni ka mare don ina ƙoƙarin yi wa ’ya’ya na tarbiya?”
“Na mare ki Fauziyya Abubakar Turaki! Ko za ki rama ne? Kin san Allah, zan iya sakin ki a kan ’ya’ya na, na gwammaci in ƙara aure ko kuma in nemo masu reno! Tafiyar ki Akeela!”
Sai da Akeela ta kalli Momma sannan ta kalli Daddy jikinta duk a sake, sai kuma ta juya da sauri ta fice daga ɗakin.
Momma kuwa da ƙarfi ta soma kiran sunanta tana faɗin,
“Akeela nooo! Ki dawo gida, kin san fa ba ki iya driving sosai ba. Don Allah ki dawo gida!”
Amma Akeela ko juyowa ba ta yi ba.
Daddy kuwa ko kallo ɗaya bai ƙara yi mata ba ya wuce, yayin da su Shuraim suka gama dariyarsu suma suka haura sama.
Momma kuwa da ƙyar, da ja jikinta tana kuka, ta wuce ɗakinta, ta kulle ƙofa tare da rushewa da kuka.
________________________________________
AFTER FOUR HOURS
Wayar Daddy ce ta yi ƙara. Har bacci ya soma ɗaukar sa, ya kai hannu ya lalubi wayar. Ganin wacce ke kira ya yi saurin picking tare da faɗin,
“Akeela my love!”
Shassheƙar kukan Akeela ya sa ya duro daga kan gado tare da faɗin,
“What’s happening Akeela? Why are you crying?”
A firgice yake tambayarta kamar yadda ita ma take kuka da iya ƙarfin ta tana faɗin,
“Daddy help me! Police sun kama ni, na bige wani mutum kuma ya mutu! Ga su nan za su tafi da ni police station!”
Da ihu yake magana yana faɗin,
“Kina ina? Kuna ina yanzu? Ki ba ɗaya daga cikin su in yi magana da shi. Ina za su kai min ke? Calm down Akeela, I won’t let anything happen to you. Stop crying, right. Your daddy will be there soon.”
Duk yana maganar ne yana tafiya dif-dif-dif har ya isa ƙofar ɗakin Momma da ta yi fushi ta tafi ɗakinta ta rufe ƙofa.
Kuna sauraron littafin: D’AN FAARI
Daga: Hausa Novel Dot Com
Kada ku manta ku yi:
Follow
Like
Share
Mun gode.

Irin bugun da yake wa ƙofar ya sa hankalin Momma ya tashi sosai, domin ta san tabbas babu lafiya. Domin ta riga ta sani, idan suka yi faɗa a kan ’ya’ya, ba shi yake neman ta ba, ita ce da kanta idan ta sauko take neman sa. Kuma dama ba ta yi bacci ba, tana jiran dawowar Akeela.
Da sauri ta buɗe ƙofar, ganin shi da waya a hannu yana magana da ihu-ihu, kuma ga dukkan alamu da jami’an tsaro yake magana, sai ta ji duk hankalinta ya tashi.
Yana katse wayar ta shiga faɗin,
“Dear me ya faru? Akeela ce ko? Na shiga uku, what happened to her?”
“Ki ɗauko hijab ɗinki. Akeela tana hannun police, wai ta bige wani da mota kuma wanda ta bige ɗin ya mutu!”
Hannu Momma ta ɗaura a kai tare da rushewa da kuka.
Da wani irin tsawa Dad ya ce,
“Come on ki wuce ki ɗauko mayafinki mu wuce! Nothing will happen to my daughter. Kin wani ɗaura hannu kina wa mutane ihu tare da pretending kamar kina wani son ta ne.”
Da sauri Momma ta koma ciki ta ɗauko hijab ɗinta, suka fita tare da Dad ɗin a motarsa…

TUSHEN LABARI
Gida ne irin na ƙasa wanda ko arzikin penti babu, kana hango tsurar bulo ɗin ƙasan a zahiri. Gidan ba wani babba ba ne sosai, duk da kasancewar filin gidan rabin filoti ne, amma ɗakuna huɗu ne kawai a gidan ciki ɗai-ɗai.
Malam Bawa shi ne mai gidan. Matansa na aure uku, sai mahaifiyarsa dake zaune a gidan tare da su kasancewar mijinta, mahaifinsa, ya jima da rasuwa.
Mama Ladi ita ce matarsa ta farko, tana da ’ya’ya huɗu kacal.
Ahmad shi ne ƊAN FAARI, sai Abubakar, Lawal, da kuma Umar.
Bayan Mama Ladi sai Inna Murja, ita kuma ’ya’yanta biyu ne, Sa’adatu da Sakina.
Sai ta ukun Mama Abu, ita kuma ba ta taɓa haihuwa ba.
Gaba ɗaya a gidan, Ahmad shi ne babba. Mahaifinsu ba wani mai ƙarfi ba ne, irin mutanen ne da ba sa iya ciyar da gidansu sau uku a rana saboda lalurar babu.
Haka yake tun fil azal. Gidan da yake ciki ma gadonsa ya yi wajen mahaifinsa, kasancewar shi ne ɗansa tilo.
Malam Bawa yana da faɗa sosai. Sam baya overlooking akan al’amuran gidansa. Mafadaci ne irin na bugawa a jarida.
Da Allah ya ba shi matar farko, sai ya samu masu hali. Domin kuwa Mama Ladi irin way’ennan matan ne masu masifar haƙuri, kau da kai da kuma sanyin hali. Ko magana ba ta cika yi ba. Shi ya sa a gidan ake cuta mata.
Idan aka cire Mama Abu, wacce ta kasance mafadaciya sosai amma sai an taɓo ta, bata faɗa for no reason.
Kullum idan ka ji muryoyi biyu na tashi a gidan, to Mama Abu ce da Malam Bawa. Baya raga mata, haka ita ma bata ragar masa.
Cewa take:
“NI BA JAKAR MAGINIYA BACE, CI BAI ISHE NI BA, TSIKARI YA ISHE NI!”
Inna Murja kuwa uwar husuma ce ita. Idan ka ga mata sun cika gida ana “fito ki maimaita abin da kika ce”, to ka tabbata da Inna Murja ake yi.
Sam ba ta zama ba tare da ta yi munafuncin wani ba. Idan kuma suna zaune su da yawa a waje, ɗaya na tashi, za ta hau tseguminta, ko kuma a zauna a yi gulmar wata da ita.
Ana watsewa sai ta zari mayafi ta tafi har gidan matar ta zayyane mata ƙarya da gaskiya, sannan ta nuna ita ba ta ce komai ba.
Ga kuma ɗan hali — yanzu ka aje abu, yanzu ta ɗauke. Kamar mai wankin ido.
Idan ta san akwai kuɗi a jikinka, to fa sunanka sorry, domin sai ta san yadda ta yi ta tatike ka tass.
Sannan idan za a yi caje, ko ina za a duba a jikinta ba za a taɓa ganin kuɗin nan ba, alhali kuma yana jikinta.
Hakan ne ya sa wasu da dama ba su gane tana sata ba, sai ’yan kaɗan daga cikinsu.
Kuma a hakan ita ce matar so a wajen Malam Bawa da mahaifiyarsa Daada.
Saboda ita abun hannunta a buɗe yake. Amma a wajen Daada da kuma Malam Bawa, wannan dalilin ne ya sa yake ganin duk cikin matansa babu mai ƙaunarsa kamarta.
Domin idan yana son kuɗi, kai tsaye wajenta yake zuwa ya noƙe yana ’yar murya. Ita kuma a cikin na jama’a da ta yi wuuf da shi take tsungula masa wani abu, shi da mahaifiyarsa, don ta ƙara fari a idanunsu…
Kuna sauraron littafin: D’AN FAARI
Daga: Hausa Novel Dot Com
Kada ku manta ku yi:
Follow
Like
Share
Mun gode.
Da gudu yaro ɗan shekaru biyar ya shigo gidan yana kuka da ihu, tare da soshe-soshen jiki yana faɗin:
“Inna ki taimaka min zan mutu! Wani abu na cizo na a cikin riga! Ki taimaka min Innar mu!”
Ahmad ya faɗi tare da riƙe hannun Inna, amma ko ɗagowa ba ta yi ba ta ci gaba da shararta.
Hannunta da ya riƙe ta fizge da ƙarfi tare da hankaɗa shi gefe tana faɗin:
“Abin da yake cizon naka ya kashe ka! Ni na tura ka wajen da abin yake? Ko kuwa ni na saka abin da yake cizon naka ya cije ka?”
Duk maganar nan da take yi ko kallo ɗaya ba ta masa ba, balle ta ga halin da yake ciki.
Sai sakin tsintsiya ta yi tare da shigewa ɗakinta, ta sauke labule.
Shi kuwa Ahmad, ɗakin ya faɗa yana kuka yana faɗin:
“Innar mu don girman Allah ki duba min taguwata, wasu abu cizona suke a ciki!”
Wuuull!
Ta wulloshi tun daga cikin ɗakin har waje. Sai da kanshi ya ƙumu da ƙasa, hannunsa ya juya tare da bada sautin ƙass.
Ya saki wani irin gigitaccen ƙara, sai da gidan ya ɗauka yana faɗin:
“Wayyooo! Innar mu hannuna ya karye!”
Ko leƙowa ba ta yi ba, balle ta ga halin da yaron yake ciki.
Inna Murja kuwa tana zaune daga ƙofar ɗakinta, tana yankan farce tare da taunar cingam.
Daada kuma na ɗakinta.
Inna Abu kuma ba ta gidan — ta tafi kasuwar Laraba, kasancewar tana saide-saide a gidan danginsu: barkono, kanwa, magi, gishiri, kubewa, kuka, ashana, farin magi da sauran su.
Kuma duk Laraba take fita ta saro. Da shi take ɗaukar buk’atunta.
Yayin da Inna Ladi ke sai da manja, mangyaɗa da wake.
A cikinsu Inna Murja ce kawai mai zaman banza. Sai idan an kyallara ido an ga na wasu ayi wuff da shi.
Ko ɓera baya nuna mata sata da jin ƙamshin kuɗi ba…
________________________________________
“To ni me zan maka? Uwar da ta haife ka ma bata damu da kai ba, balle kuma Murja karere. Ta ma kashe ka, wa yayi asara idan ba ita ba.”
Faɗin Murja dai-dai lokacin da wata mata ta shigo da bokiti a hannu domin jan ruwa a rijiya.
Kasancewar suna da rijiya, kuma ruwan gidan irin mai kyau ne — sam bai ƙafewa. Idan an kwashe shi tsaf, bashi minti talatin zai sake tsattsafowa.
Da sauri ta nufi inda Ahmad yake kwance tana rabga salati.
Ɗago shi ta yi, wani salatin ta ƙara rafgawa ganin hannunsa na lilo alamar karaya.
“Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un! Gaskiya Murja baki da imani. Kina ganin yaro ya yi wannan faɗuwar amma kina zaune kina kallonsa? Ɗan mijinki ne fa shi! Ai ko ba ki yi don Laadi ba, ki yi don shi Malam Bawa ko!”
Harara Inna Murja ta watsa mata tare da miƙewa tsaye tana tafiya tana faɗin:
“Ahayyee! Yau na ga ikon Allah! To ita uwar tasa da ta tsuguna ta haife shi, ta kuma san zafinsa, ita ta wurgo shi wajen har ya samu rauni a hannu kuma tana ciki tana jin ki — sai ni ’yar karere ce zan kwashi jiki in zo in taimaka masa?
Ba ki da hankali Safara’u.
Idan za ki ajiye shi a wajen, ki zo ki ɗauki bokitinki ki ja ruwa ki yi gaba to. Idan kuma za ki tsaya a wajen kina baɓatu, to ni kin ga shigewa ta ɗaki.”
Tana gama faɗin haka ta ɗaga labule ta faɗa ɗaki har da turo ƙyaure…
________________________________________
Safara’u kuwa, Ahmad a hannunta yana ihu, ta ɗaga labule ko sallama ba ta yi ba, ta faɗa ɗakin Inna Ladi tana faɗin:
“La haula wala quwwata! Dama da gaske Laadi kina cikin ɗaki kina jiyo irin wannan ihun neman taimako da ɗan nan yake yi?
Haba Laadi! Wannan wani irin mummunar al’ada ce haka? Ɗanki ne fa!
Dubi halin da yake ciki fa!”
Ta faɗi tana mai yin nuni da lankwashasshen hannun Ahmad.
Inna Ladi dake zaune bakin gado tana ninke kayan su Abubakar da ta kwaso daga shanya kafin ta fara shara.
Ko kallon inda Safara’u take ba ta yi ba.
Sai ma tsam da ta yi ta tashi daga kan gadon, tare da yin wuff ta fito daga ɗakin ta bar Safara’u da sakakken baki, riƙe da Ahmad a hannunta.
“Na shiga uku ni Safara! Wannan wacce irin uwa ce? Ko zamanin kakanni anya akwai irin su kuwa?
Ka jeho ɗanka da kanka har ya karye, amma ko a jikinka — saboda kawai ya kasance ƊAN FAARI!
Idan kunya ce tuni kika zubar tunda har kika iya tuɓewa a gaban ubansa har ya ɗora miki ciki kika haife shi.
Akwai wani rashin kunya da ya wuce wannan?
Tun da duk wanda ya gan ki da ɗa ya san abin da kika yi kika haife shi!”
Tana gama faɗin haka ta kwantar da Ahmad nan ƙasa a ɗakin, ta fice tana faɗin:
“Ba ruwana billahil kada in taka sawun ɓarawo. Yaro ya zo ya mutu a hannuna daga zuwa ɗiban ruwa, ace ni na kashe shi hukuma ta ɗaure ni.
Ni wallahi ɗibar ruwan ma na fasa…”
Sai mun haɗu a next page. But comment, Like da kuma Share ɗin ku shi ke Sani Jin Karsashin yin saurin suburbuɗo muku wani page ɗin!

Pages: 1 2 3 4
Uncategorized

Post navigation

Previous Post: GIDAN UNCLE Complete

Related Posts

GIDAN UNCLE Complete Uncategorized

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Archives

  • April 2026

Categories

  • Uncategorized

Recent Posts

  • D’AN FAARI Complete
  • GIDAN UNCLE Complete

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on GIDAN UNCLE Complete

Copyright © 2026 Hausa Novel.

Powered by PressBook Masonry Blogs

Powered by
►
Necessary cookies enable essential site features like secure log-ins and consent preference adjustments. They do not store personal data.
None
►
Functional cookies support features like content sharing on social media, collecting feedback, and enabling third-party tools.
None
►
Analytical cookies track visitor interactions, providing insights on metrics like visitor count, bounce rate, and traffic sources.
None
►
Advertisement cookies deliver personalized ads based on your previous visits and analyze the effectiveness of ad campaigns.
None
►
Unclassified cookies are cookies that we are in the process of classifying, together with the providers of individual cookies.
None
Powered by